Da ka nake rera kusan dukkan wakoki na - Ado Gwanja

Da ka nake rera kusan dukkan wakoki na - Ado Gwanja

Sanannen mawaki kuma jarumi a masana'antar Kannywood, Ado Gwanja ya tabbatar da cewa ya rera wakoki kusan 600 tunda ya fara sana'ar waka.

Jarumin ya ce da yawa daga cikin wakokin da kansa ya rera ba tare da ya rubuta su ba.

Fitaccen mawaki Ado Gwanja ya sanar da hakan ne a hirar da yayi da BBC Hausa Instagram Live a ranar Alhamis da ta gabata.

Da aka tambaya mawakin matan ko waka na wahalar da shi, sai ya ce "A gaskiya babu abinda ke bani wahala" matukar ya zo rera waka.

"Idan na kira makidi nace masa ya buga min kida iri kaza, ko yanayin nayi mishi bayani, ina cikin ji wakar take zuwa.

"Daga nan na kan ce a samo min furodusoshi kawai," cewar jarumi kuma mawaki Ado Gwanja.

Kamar yadda Ado Gwanja ya sanar, ya ce a cikin wakoki 600 da yayi, ba su wuce biyu daga ciki ba da ya rubuta ba.

Su ma kuwa saboda bashi shawara da aka yi ne yasa ya rubuta wakokin, amma ba don ya saba yin hakan ba.

Ya ce wakar farko da ya rera ita ce Gawasa. Kuma ko bayan da ya rera ta shi aka bari da kayansa ya dinga jinta har ta isheshi.

Wakokin mawaki Gwanja da suka yi sharafi sun hada da: Kujerar Tsakar Gida, Asha Ruwa da Salon Kida.

Da ka nake rera kusan dukkan wakoki na - Ado Gwanja
Da ka nake rera kusan dukkan wakoki na - Ado Gwanja. Hoto daga BBC
Asali: Getty Images

KU KARANTA: 'Yan sanda sun damke korarren dan sandan da ya kware wurin satar babur

Fitaccen mawakin ya ce banda sana'ar waka, babu sana'ar da ke burgesa kamar ta shayi

"Mu asalin gidanmu sana'arsu shayi, ko mace ko namiji, hatta iyayenmu da sana'ar shayi aka auro su," in ji Gwanja.

Fitaccen mawakin ya ce ya daina fitowa a matsayin dan daudu a fim saboda matarsa yake so ta dinga yin dariyarta ta fadi tare da tashi.

Tun a baya ya sanar da BBC Hausa cewa yadda ya kware a kwaikwayon 'yan daudu ne yasa ake sa shi fitowa a abinda ya danganci hakan.

Ado Gwanja dan asalin Kofar Wambai ne ta jihar Kano. Mahaifinsa fitaccen mai shayi ne wanda ake kira Gadagi Mai Shayi.

Ya yi karatu har zuwa matakin sakandare. Yana da matar aure daya da 'ya daya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel