Bayan dogon jira, fim din 'Gidan Badamasi' zango na 4 zai shiga kasuwa nan kusa

Bayan dogon jira, fim din 'Gidan Badamasi' zango na 4 zai shiga kasuwa nan kusa

  • Masu shirya fim din Gidan Badamasi sun yi bayanin lokacin da za a saki shirin mai dogon zango da aka jima ana jira
  • Falalu Dorayi, wanda ya shirya fim din ya kuma bayyana yadda aka samu sabbin sauye-sauye a cikin shirin
  • Hakazalika, ya kuma ce an samu sabbin fitattun jaruman Kannywood domin karawa shirin armashin gaske

Kaduna - Shirin wasan barkwanci na Gidan Badamasi zango na 4, wanda ake jira shine zai zai shigo kasiwa a ranar 6 ga Janairu, 2022, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Malam Falalu Dorayi, wanda shi ne ya shirya shirin, ya ce zango na 4 zai fi armashi fiye da na baya domin an sake samo sabbin taurari masu barkwanci da karin kwararrun ma’aikata fiye da da.

Mai shirya fim din Gidan Badamasi, Falalu Dorayi
Bayan dogon jira, fim din 'Gidan Badamasi' zango na 4 zai shiga kasuwa nan kusa | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Falalu ya kuma bayyana cewa an dauki shirin a wurare daban-daban a jihar Kaduna kuma an cusa wasu sabbin sassa masu ban sha'awa a cikin shirin domin kayatar da masu kallo.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Minista ya bayyana hanyar da Buhari zai bi wajen sakin Nnamdu Kanu

Ya bayyana cewa shirin na daya daga cikin fina-finan Hausa masu dogon zangi da suka samu karbuwa a wurin jama'a saboda haka shirin mallakin al'umma ne.

A cewar Dorayi:

"Gidan Badamasi zango na 4 zai kasance shiri mai ban sha'awa, daga farko, mun amince da karbar shawarwarin masu kallo kuma hakan ya sanya shirin ya zama abin son jama'a."

Zango na 4 yana dauke da jarumai irinsu Hadiza Gabon, Adam A Zango, Naburuska, Bosho, Dan Kwambo, Falau A Dorayi da sauran fitattun jaruman Kannywood.

Legit.ng Hausa ta ziyarci shafin Instagram na Falalu Dorayi, inda taga sanarwa kamar haka:

"Barkanmu da Shekarar Miladiyya (2022) In shaa Allah #GidanBadamasi4! zai dawo muku 6 January 2022, ranar Alhamis, A tashar @arewa24channel 8:00 na dare."

Jaruma Nafisa Abdullahi ta sanar da ficewa daga fim din Labarina, ta sanar da dalilanta

Kara karanta wannan

Bidiyon matasan da suka shiga hannu yayin da suke kokarin yin asirin kudi da wata budurwa

A wani labarin, Fitacciyar jarumar Kannywood kuma tauraruwar shiri mai dogon zango na Labarina, Nafisa Abdullahi, ta sanar da ficewarta gaba daya daga shirin fim din.

Tun farko, an yi makonni ba a ga jarumar ta bayyana cikin shirin ba sakamakon yadda wasan ya zo na cewa an yi garkuwa da ita, lamarin da yasa masoyanta suka dinga guna-gunin rashin bayyanarta.

Sai dai a ranar 1 ga watan Janairun sabuwar shekara, jaruma Nafisa Abdullahi ta wallafa takarda a shafin ta na Instagram inda ta sanar da cewa ta fice daga shirin sakamakon tarin ayyukanta da karatu da ya sha mata kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel