Har yanzu ina nan ban yi bankwana da Kannywood ba - Hadiza Kabara

Har yanzu ina nan ban yi bankwana da Kannywood ba - Hadiza Kabara

- Fitacciyar jaruma Hadiza Muhammad Sani wacce aka fi sani da Hadiza Kabara ta ce ba ta bar harkar fim ba

- A cikin kwanakin nan ne aka hango tsohuwar jarumar a wasu fina-finai masu dogon zango da suka hada da 'Gidan Badamasi' da kuma 'Dadin Kowa'

- Jarumar ta ce da wannan harkar suka yi wayau kuma suka budi ido, don haka ba zasu ce zasu fice ba

Sananniyar jaruma Hadiza Muhammad Sani wacce aka fi sani da Hadiza Kabara ta ce har yanzu ba ta yi bankwana da masana'antar Kannywood ba.

Jarumar ta sanar da hakan ne a lokacin tattaunawarta da mujallar fim ta Fim Magazine.

A hirar da aka yi da Hadiza, ta ce "ban ce na yi bankwana da harkar film ba saboda da ita muka yi wayau kuma muka budi ido. Don haka ba za mu iya bakwana da harkar ba."

KU KARANTA: Miji ya yiwa matarshi karyar ya mutu saboda tambayarshi kudi da take

Jarumar ta ce an samu sauyi a harkar gudanarwa idan aka danganta da shekarun da suka shude. A halin yanzu akwai karancin aikin ba kamar yadda ake yi a baya ba.

"A yanzu sai ka ga an dade ba a shirya fim ba saboda yadda kasuwar siyar da fina-finan ta yi kasa."

Tsohuwar jarumar ta kara da cewa, "yanzu an fi yin fina-finai masu dogon zango wadanda ake kallo a manyan gidajen talabijin. Don haka abinda zan iya cewa shi ne harkar ta zama sai addu'a."

Hadiza ta bayyana cewa bayan dawowarta masana'antar, ta yi fina-finai da dama amma 'Gidan Badamasi' da 'Dadin Kowa' ne suka fara fitowa.

Ta nuna jin dadinta ta yadda masoyanta suka kara karbarta a harkar hannu bibbiyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel