Hotuna: An yi jana’izar shahararren jarumin Kannywood, Umar Malumfashi, Ya Yi Jama’a Sosai

Hotuna: An yi jana’izar shahararren jarumin Kannywood, Umar Malumfashi, Ya Yi Jama’a Sosai

  • An yi jana'izar fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Umar Malumfashi, a jihar Kano
  • Marigayin wanda aka fi sani da Ka fi gwamna a shirin Kwana Casa'in ya kwanta dama a daren ranar Talata, 27 ga watan Satumba
  • Gomman jama'a ciki harda manyan abokan sana'ar marigayin sun samu halartan jana'izarsa wanda aka yi a safiyar yau Laraba

Kano - A safiyar yau Laraba, 28 ga watan Satumba ne aka gudanar da jana’izar shahararren jarumin nan na masana’antar shirya fina-finan Hausa, Umar Malumfashi, a jihar Kano.

Dandazon jama’a da manya-manyan jaruman masana’artan sun samu halartan jana’izar marigayin inda aka sada shi da gidansa na gaskiya.

Jana'iza
Hotuna: An yi jana’izar shahararren jarumin Kannywood, Umar Malumfashi, Ya Yi Jama’a Sosai Hoto: bbchausa
Asali: Instagram

Fitattun abokan marigayi Umar Malumfashi cikinsu har da Salisu T. Balarabe daya daga cikin daraktocin fitaccen fim din Kwana Casa'in, inda jarumin ya ci sunan Ka-fi-gwamna sun halarci jana'izar a Kano.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Fitaccen Jarumin Kannywood Na Shirin Kwana Casa'in, Kafi Gwamna, Ya Rasu

Daga cikin manyan abokan sana’ar marigayin da suka sallaci gawarsa harda Salisu T. Balarabe daya daga cikin daraktocin fitaccen fim din Kwana Casa'in, wanda a cikin fim din ne jarumin ya ci sunan Ka-fi-gwamna, BBC Hausa ta wallafa a Instagram.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran manyan iyaye a masana’antar kamar su Tahir Fagge, Alhaji Hamisu Iyantama da Baba Sogiji duk sun halarci jana'izar abokin sana’ar tasu.

A daren ranar Talata, 27 ga watan Satumba ne aka samu labarin mutuwar marigayin wanda ya taba masoya da dumbin masu son kallon fina-finansa.

Kannywood: Gaskiyar Dalilin Da Ya Sa Naje Gidan Gala Har Na Taka Rawa Da Yan Mata, Tahir Fage

A wani labarin, Shahararren jarumin masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Tahir I. Fage, ya bayyana dalilinsa na zuwa gidan gala harma ya taka rawa.

Jama’a dai suna ta yamutsa gashin baki bayan bayyanar bidiyon jarumin wanda ya dade ana damawa da shi inda suka dunga sukarsa kan rawa da ya yi da wasu yan mata, cewa sam ba girmansa bane.

Kara karanta wannan

Abin da ake fada a shafin sada zumunta a kan ‘haduwar dolen’ Kwankwaso da Ganduje

Sai dai a wata hira da ya yi da Sashen Hausa na BBC, Tahir Fage ya bayyana cewa rashin kudi ne ya same shi, ga rashin lafiya shi ya sa ya je ya yi rawar domin ya samu na magani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel