Abin da ake fada a shafin sada zumunta a kan ‘haduwar dolen’ Kwankwaso da Ganduje

Abin da ake fada a shafin sada zumunta a kan ‘haduwar dolen’ Kwankwaso da Ganduje

Abuja - Legit.ng Hausa ta fahimci an yi wani irin gamo tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Rabiu Musa Kwankwaso.

Wani hoto da aka yada a shafin Twitter a ranar Litinin, 26 ga watan Satumba 2022, ya nuna Rabiu Kwankwaso ya ci karo da magajinsa

Hassan Sani Tukur wanda aka sani da Nobel_Hassan ya wallafa hoton a shafinsa, yake cewa filin jirgi mai hada zumuncin dole.

Bayan Dr. Abdullahi Ganduje ya zama Gwamnan Kano, an samu sabani tsakaninsa da Rabiu Kwankwaso wanda shi ne mai gidansa.

Bayan mutane sun ga hoton, sun yi ta tofa albarkacin bakinsu a dandalin sada zumuntan.

Kwankwaso da Ganduje
Sanata Kwankwaso da Gwamna Ganduje Hoto: @Noble_Hassan
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

El-Rufai Ya Girgiza da Jin Abin da Peter Obi Yake Fada Domin Jawo Kuri’un Kiristoci

Siyasar Kano sai Kano

Wani ‘dan jam’iyyar APC kuma masoyin Gwamna Ganduje, Ahmad Gogel yake cewa:

“Kana ganin zaman kasan waye mai zaman defo”

Shi ma Ahmad Muhammad, a cikin raha, ya rubuta:

“Kana ganin zaman kasan waye babba, Lol”

- Ahmad Muhammad

Naga oga yana rufe aljihu SA da hannun SA me yake nufi ne wai

- Mansur Kabara

Shi kuma Saleh Sanusi Minjibir ya bayyana abin da ya lura da hoton, yace Kwankwaso ya zurawa Ganduje kallo har ido, shi kuwa Gwamnan ya kauda idanunsa.

Yakubu AYB yace darasin da za a dauka shi ne ka da mutum ya yi fada saboda ‘yan siyasa, domin a je a dawo, suna tare da juna.

Wani mai sunan Baban Zara ya rubuta:

“Na ciki, na ciki.”

Yahaya M. Salisu yace wadannan mutanen ba fada suke yi ba fa!

Wata Amina Ishaq tambaya take yi ko abokan gaban sun yi magana da junansu.

Kara karanta wannan

Da Gaske Aure Za Su Yi? Hotunan Hauwa Ayawa da Umar Gombe Ya Haddasa Cece-kuce A Soshiyal midiya

Amaechi da Wike

Shi kuma wani yake cewa ba za a taba ganin wannan tsakanin Gwamnan jihar Ribas watau Nyesom Wike da tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ba.

Da farko Nyesom Wike da Amaechi aminai ne a siyasa. Yayin da Wike ya zama Minista a gwamnatin Jonathan, Amaechi ya koma APC a 2014.

Lissafin zaben Shugaban kasa

Dazu kun samu rahoto nan da ‘yan watanni ‘Yan Najeriya za su samu kansu wajen kada kuri’u a zaben sabon shugaban kasa wanda zai mulki kasar nan.

Mun fahimci za ayi amfani da dukiya, kabilanci da sabanin addini wajen karkato da hankalin masu kada kuri’a. Rabiu Kwankwaso yana cikin ‘yan takaran.

Asali: Legit.ng

Online view pixel