Jarumin Kannywood, Umar Malumfashi, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Jarumin Kannywood, Umar Malumfashi, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Duk mai rai wata rana zai koma ga Allah, Jarumin Kannywood, Umar Malumfashi, ya riga mu gidan gaskiya da yammacin nan
  • Marigayin, wanda aka fi sani da Kafi Gwamna a shirin Kwana Casa'in mai dogon zango ya rasu ne a wani Asibiti a Kano
  • Bayanai sun nuna cewa za'a gudanar da Jana'izarsa kamar yadda Musulunci ya tanada gobe da karfe 9:00 na safe a gidansa na Hotoro

Kano - Rahoton da muka samu yanzu ya nuna cewa jarumin masana'antar Kannywood, Umar Malumfashi, wanda aka fi sani da Yakubu Kafi Gwamna a Shirin Kwana Casa'in, ya rasu.

Ɗaya daga cikin jaruman masana'antar, Abba El-Mustapha, shi ne ya sanar da rasuwar a shafinsa na dandalin sada zumunta Instagram.

Kara karanta wannan

Abin da ake fada a shafin sada zumunta a kan ‘haduwar dolen’ Kwankwaso da Ganduje

Umar Malumfashi.
Jarumin Kannywood, Umar Malumfashi, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Hoto: @abbaelmustapha1
Asali: Instagram

Marigayin ya rasu ne a wani Asibitin dake Anguwar Hausawa, kusa da masallacin Murtala a kwaryar birnin Kano yau Talata 27 ga watan Satumba, 2022 bayan sallar Magriba.

A cewar Abba El-Mustapha, za'a gudanar da jana'izar marigayin gobe Laraba a gidansa dake Hotoro da misalin ƙarfe 9:00 na safe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jarumi Abba yace:

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allah ya yi wa babanmu, Alhaji Umaru Malumfashi, wanda aka fi sani da KAFI GWAMNA rasuwa. Za'a yi jana'izarsa a gobe a Unguwarsu ta Hotoro da karfe 9:00 na safe."
"Muna addu'ar Allah ya jiƙansa ya gafarta masa kurakuransa, ya sa Aljanna ce makomarsa. Idan ta mu ta zo Allah ya sa mu cika da kyau da Imani."

Marigayin ya shahara da sunan Kafi gwamna ne saboda rawar da ya taka a shirin Kwana Casa'in mai dogon zango wanda kafar Talabijin ta Arewa 24 ke haskawa.

Kara karanta wannan

Bayan Atiku Ya Kammala Wa'adin Mulkiinsa, Kudu Maso Gabas Ce Zata Samar da Shugaban Kasa, Jigon PDP

Makusancin shugaba Buhari ya kwanta dama

A wani labarin kun ji cewa Makusancin Buhari, Tsohon Kakakin CPC Kuma Darakta a NIMASA, Ya Kwanta Dama

Makusancin shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma tsohon daraktan ayyuka na hukumar NIMASA, Rotimi Fashakin ya kwanta dama.

Kafin rasuwarsa, ya taba kasancewa kakakin tsohuwar jam'iyyar CPC kuma jigon jam'iyyar APC a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel