Gaskiya Mijinki Ya Iya Kiwo: Hotunan Matar Aure Na Da da Yanzu Ya Haddasa Cece-kuce

Gaskiya Mijinki Ya Iya Kiwo: Hotunan Matar Aure Na Da da Yanzu Ya Haddasa Cece-kuce

  • Wata matashiyar yar Najeriya mai suna Juliet ta haddasa cece-kuce a shafin soshiyal midiya bayan ta nuna yadda ta sauya gaba daya shekaru bayan aurenta
  • Juliet ta wallafa wani tsohon hoto na yadda take a lokacin da ta shiga gidan miji da kuma yadda take a yanzu bayan ta haifi yara uku
  • Jama’a sun jinjinawa mijinta yayin da suka yaba da yadda ta sauya ta kara kyau kamar ba ita ce ta haifi yara uku ba

Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan ganin hotunan yadda wata matashiya ta sauya gaba daya bayan ta yi aure da sahibinta.

Matar mai suna Juliet ta je shafinta na TikTok don wallafa wani tsohon hotonta don nuna yadda kamanninta suke a lokacin da take sabuwar amarya.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yaro Ya Tsokani Mahaifiyarsa Mai Juna Biyu, Ta Daura Masa Kwallon Kankana Don Ya Ji Yadda Abun Yake

Matar aure
Gaskiya Mijinki Ya Iya Kiwo: Hotunan Matar Aure Na Da da Yanzu Ya Haddasa Cece-kuce Hoto: TikTok/@julietsignature
Asali: UGC

Fatar jikin Juliet na da dan duhu kuma bata da jiki a hoton. Sai dai kuma, sabon hotonta ya nuna yadda ta sauya gaba daya ta kara wani irin kyau.

A yanzu da take da yara uku, fatar jikin Juliet ta kara haske sosai sannan ta yi cikar daki sosai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta wallafa hotonta ita kadai cikin gayu sannan ta wallafa wasu da ta dauka tare da iyalinta.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama'a

Phatima ta ce:

"Kin auri mutumin kirki kuma na yarda cewa kema kina iya bakin kokarinki. Allah ya karo maku shekaru a tare za ku tsufa tare insha Allah."

user9012677564446 ya ce:

"Mijinki ya cancanci a bashi lambar yabo.
"Na rantse.
"Dubi baya da yanzu."

Confam Queen ta ce:

"Ya zama dole mu tafi gidanmu kuma gida mai kyau za mu shiga ba wanda zai sa mu fi mahaifiyarmu tsufa ba."

Kara karanta wannan

Yan Baiwa: Bidiyon Wasu Kyawawa Yan Gida Daya Da Duk Jikinsu Gashi Ne Har Fuska

Bidiyon Yadda Amarya Ta Zage Ta Kwashi Garar Girki Kafin Ta Shiga Filin Rawa

A wani labarin, yawanci idan ana shagulgulan aure ba a damu da baiwa amare abinci ba a wannan rana ganin cewa saboda su ne aka tara jama’a.

Hankula sun fi karkata wajen tabbatar da ganin baki da aka gayyata sun ci sun sha yadda ya kamata. Wasu har sai ka ga amaren sun jigata basu da wani kuzari saboda ciki bai dauka ba.

Sai dai wata amarya ta sauya wannan al’ada inda aka haskota tana kwasar girki. An gano ango zaune a gefenta yayin da ita kuma take ta aika loman abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel