Bidiyoyin Cikin Dankareren Gidan Da Jaruma Sadiya Haruna Ta Ginawa Mahaifiyarta

Bidiyoyin Cikin Dankareren Gidan Da Jaruma Sadiya Haruna Ta Ginawa Mahaifiyarta

  • Jarumar Kannywood, Sadiya Haruna ta gwangwaje mahaifiyarta da wani katafaren gida na alfarma
  • Jaruma Sadiya ta sanyawa kowani bangaren kayan alatu kama daga gadaje da kujeru na zamani, harda na'urar sanyaya waje
  • Bidiyoyin ciki da wajen dankareren gidan ya bayyana a shafin jarumar na soshiyal midiya

Jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood kuma mai daukar hankali a kafafen sada Zumunta ta Instagram, Sayyada Sadiya Haruna, ta gwangwaje mahaifiyarta.

Sadiya ta dankarawa mahaifiyar tata wani katafaren gida domin ta more tare da cin ribar haihuwarta da tayi.

Sau da dama jarumar ta sha fitowa tana bayyana irin soyayyar da take yiwa mahaifanta musamman ma mamar tata, sannan ta sha cewa a kullun cikin yi mata addu’a suke don haka ita ma take son farin cikinsu.

Sadiya Haruna
Bidiyoyin Cikin Dankareren Gidan Da Jaruma Sadiya Haruna Ta Ginawa Mahaifiyarta Hoto: sayyada_sadeya_haruna
Asali: Instagram

Jarumar ta wallafa bidiyoyin cikin gidan da ta kerawa mahaifiyar tata sannan ta bi koina daki-daki tana yiwa masoyanta bayanin kowani bangare na gidan.

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata Budurwa Yayin Da Ta Yi Cikibis Da Matar Da Ta Raine Ta Bayan Shekaru 25

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta fara da hasko cikin dakinta wanda ta jerawa kayan alatu da katafaren gado da kwaba irin na zamani, sai kuma bandaki da na’urar sanyaya daki.

Daga nan sai ta garzaya bangaren da aka tanada na musamman don cin abinci, inda yake dauke da kujeru da teburin cin abinci, sai kuma falo wanda ke dauke da kujerun alfarma irin na zamani.

Sadiya ta kuma hasko bidiyon bangaren da ta tanada domin diyarta Khadija inda itama aka saka mata dan madaidaicin gado da kwaba da kuma na’urar sanyaya daki, shima dai da bandakinta ciki.

Sai bangaren mahaifiyarta in da aka gano mamar tata zaune a kan gadon zamani da aka saka mata da kwabanta da na’urar sanyaya daki, shima dai akwai bandaki a ciki.

Bayan nan ta zagaya bangaren baya wanda aka yi wasu dakuna da ya fi kama da na yara maza jere. Komai dai ya ji dagwas-gwas a gidan.

Kara karanta wannan

Yadda Malamar Jami’a Ta Koma Tallan Dankali Saboda Yajin Aikin ASUU

Ga jerin bidiyoyin wanda ta wallafa a shafinta na Instagram a kasa:

Jama'a sun taya ta murna

zubymuazu70 ta yi martani:

"Mashaa Allah, Allah ya Sanya alkhairi"

hajjas388 ta ce:

"Ina taya ki murna yar'uwa Allah ya kare❤️❤️❤️"

a.a.ikaka ta ce:

"Masha Allah ❤️❤️❤️Allah ya albarkace ki da mahaifiyarki"

chawoidris1 ya ce:

"Allah ya sa Albarka❤️❤️❤️❤️❤️❤️"

abdul_producer1 ya rubuta:

"Masha Allah"

Manyan Jaruman Kannywood Mata, Tsoffi Da Na Yanzu Sun Hadu A Wajen Liyafar Kungiyarsu, Sun Girgije A Bidiyo

A wani labarin, mun kawo a baya cewa kungiyar jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood mata mai suna AFAKA ta gudanar da wata kasaitacciyar liyafa kara dankon zumunci.

Taron ya samu halartan manyan jaruman fim mata na da da yanzu, inda suka sha rawa suka girgije.

A wata wallafa da shugabar kungiyar, Ambasador Rashida Adamu Albadullahi Maisa'a ta yi a shafinta na Instagram, ta bayyana cewa daga yanzu suna za a dunga damawa da su a kowani bangare.

Kara karanta wannan

An yi adalci: Mahaifin Hanifa ya yi martani bayan hukunta malamin da ya kashe masa diya

Asali: Legit.ng

Online view pixel