Bidiyon Yadda Amarya Ta cafke Dalolin Da Aka Lika Mata A Wajen Liyafar Bikinta

Bidiyon Yadda Amarya Ta cafke Dalolin Da Aka Lika Mata A Wajen Liyafar Bikinta

  • Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar bidiyon wata amarya a shafukan soshiyal midiya
  • An yiwa amaryar liki wasu yan daloli inda ita kuma ta sa hannu ta cafke abunta
  • Jama’a da dama sun goyi bayan haka, inda suka ce farashin dala ya tashi gara ta adana abunta da kanta kafin wani ya dafe

Bisa al’ada idan aka ce ana taro imma na aure ko suna a kan tanadi tawaga na musamman wadanda aikinsu a wannan wuri shine kwashe kudaden liki.

Sai dai kuma wata amarya ta shayar da mutane mamaki bayan da aka gano ta a cikin bidiyo tana cafke kudaden da ake lika mata.

Amarya
Bidiyon Yadda Amarya Ta cafke Dalolin Da Aka Lika Mata A Wajen Liyafar Bikinta Hoto: weddings_and_cruise
Asali: Instagram

A cikin bidiyon wanda ya yadu a shafukan soshiyal midiya, an gano amaryar wacce aka ambata da suna Aisha a filin rawa yayinda wata hajiya ta bude jakar hannunta ya zaro daloli tana lika amaryar.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Budurwa Ta Gwangwaje Saurayinta da Kyautar PS5 Sabo Dal

Maimakon ta bari ya zube a kasa sai kawai amarya Aisha ta sanya hannu tana wartan abunta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai mutane da dama a soshiyal midiya sun goyi bayan abun da tayi duba ga tashin farashin dala a kasuwar canji.

Kalli bidiyon wanda shafin weddings_and_cruise ya sanya a Instagram a kasa:

Martanin mabiya soshiyal midiya

comr_danmama ya yi martani:

"$ yau ga $ Hajiya $$$"

kaddycrush ta ce:

"Mata da kudi "

yusif.alhaji.779 ya ce:

"Masha Allah "

bee7th ta ce:

"Kina gaskiya rike dollar amarya kasa ta yi wahala"

mikailzeee ta yi martani:

"Kwashe yar'uwa naki ne bawani forming ko nice saina rike yasin "

maryam_umar24 ta ce:

"Gskyn rike abunki"

maims_scentsandmore ta kara da cewa:

"Omo in ni ce ai bazan jira har sai an miko min wacce ta fadi ba zan tsuguna na kwashe"

Kara karanta wannan

Bidiyon Shigowar Kasaita Da Amarya Amina Isiyaka Rabiu Tayi A Wajen Liyafar Aurenta

Yadda Budurwa Mai Shekaru 22 Ta Fada Soyayyar Tsohon Mai Shekaru 88 Har Ta Samu Juna Biyu

A wani labarin, Chibalonza ta kasance matashiya yar shekaru 22, amma kuma sai ta fada a tarkon soyayya da tsohon da ya isa yin jika da ita, wato Kasher Alphonse mai shekaru 88.

Mutumin ya fada ma Afrimax English cewa sun kasance suna son juna kuma sun fahimci junansu duk da banbancin shekaru 66 da ke tsakaninsu.

A cewar masoyan wadanda suka shafe tsawon shekaru biyu tare, sun fada a tarkon soyayya da zuciyoyinsu ne amma ba wai da shekarunsu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel