Mutane su gama aibatani a zo ranar lahira su ga na shige Aljanna na barsu - Umma Shehu

Mutane su gama aibatani a zo ranar lahira su ga na shige Aljanna na barsu - Umma Shehu

  • Jarumar masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Umma Shehu ta magantu a kan masu zaginta
  • Umma ta bayyana cewa ita zunubanta take kallo ba na mutane ba don haka bata damu da irin zagin da ake mata ba
  • Ta kuma ce Allah mai yafiya ne, cewa masu zaginta na iya zuwa a ranar kiyama su ga ta shige Aljannah wuf ta barsu a tsaye

Shahararriyar jarumar masana’antar shirya fina-finan hausa ta Kannywood, Umma Shehu, ta yi tsokaci a kan aibata ta da wasu mutane ke yi, sakamakon kallo da suke yi mata a matsayin mai aikata sabon Ubangiji.

A wani bidiyo da sashin Hausa na BBC ya fitar, an jiyo jarumar tana fadin cewa ita da zunubinta ta damu ba da na wani ba sannan kuma cewa duk a laifukan da take aikatawa bata hada Allah da wani.

Kara karanta wannan

Labarin Mary Ann: Hotunan Matar da ta fi kowa muni a duniya kuma ta ci gasar munana

Mutane su gama aibatani a zo ranar lahira su ga na shige Aljanna na barsu - Umma Shehu
Umma Shehu ta ce bata taba hada Allah da wani ba Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Jarumar ta kuma bayyana cewa tana cika salollinta guda biyar, don haka Allah mai gafara ne, idan ta roke sa cikin kuka zai yafe mata.

Ta kuma bayyana cewa kada masu zaginta su yi mamaki idan aka zo ranar tsayawa a madakata su ga ta wuce aljannah ta barsu a tsaye saboda wannan aibata ta da suke yi.

Ta ce:

“Ka san su mutane basa raina abun magana, basa raina abun zagi. Idan ka yi wa mutum abu ba daidai baa bun da nake tsammani idan mutum yana son ka, ka biyo ni ta DM ka yi mani magana wallahi zan saurare ka. Saboda menene, ai babu wanda baya kuskure, na san ni mai laifi ce kuma ni mai zunubi ce.
“Toh ka biyo ni ta DM ni narigada na gama na barsu da magana, abun gabana nake yi bana kallon abun gaban wani. Duk abun da laifin wani yake yi bana kallon shi nawa na sani. Laifi tudu ne ka take naka ka hango na wani.

Kara karanta wannan

Wata mata a Nasarawa: Dalilin da yasa na amince 'dan da na haifa ya dirka min ciki

“Duk zunubin da zan yi bana hada Allah da wani, bana shirka, ina bin Ubangiji, ina sallolina guda biyar. Wallahi na san shi gafurul-raheem ne. Idan na zauna na yi kuka na roke shi zai yafe mun zunubaina, Zai iya yafe mun.
“Kuma ina nan da uwa a raye, kullun tana yi mun addu’an Allah ya rabani da sharrin masu zagina, kullun tana yi mun addu’a Allah ya tsare ni daga sharrin masharrata, domin su masu zagin sune masharrata.
“Ni bana kallon surutun mutane ban ma san suna yi ba wallahi, ni na riga na dauki wannan a matsayin kaddarata ce. Misali kamar ni da Rahama Sadau, Rahama duk abun da za ta yi sai mutum ya je yana zaginta, kila ma ta fi ka kusanci da Ubangiji. Wallahi abu kadan za ka yi sai ya zama abun surutu, abu kadan zan yi sai ya zama abun surutu, toh na barshi a matsayin kaddara ta ce haka, kuma b azan taba kaucewa kaddara ta ba mai kyau ko mara kyau.

Kara karanta wannan

'Yar Najeriya Mai Al’aurar Maza Da Mata Ta Samu Mijin Aure Bayan Labarin Ta Ya Bazu A Kafafen Sada Zumunta

“Duk yadda Allah ya yi ni a haka nagode masa. Su yi surutunsu, su yi zaginsu, ni kuma ina a dakina ina shan ruwan sanyi na maida kai na kwanta. Saboda zagin da suke yi mun wallahi irin wannan zagin sai ka gani ina mutuwa, ina tsaye da ku a madakata, sai ku ga na wuce ku, na tafi na barka saboda kowa ta-kai ta-kai, zagin nan sai an dauko ladanka an bani kuma ko ka ki Allah sai na amsa. Na barka a wajen bincike ni na rigada na wuce, don haka zagi baya kari. Ka taba ji ance zagi ya kashe wani?, wallahi baya kisa don haka kada su daina suyi ta yi.”

Kalli bidiyon a kasa:

Ana yawan yi mun gori da na ki yin aure amma na san Allah bai manta da ni ba - Fati Slow

A wani labarin, fitacciyar tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Fati Usman wacce aka fi sani da Slow Motion ta bayyana cewa mutane na yawan yi mata gori kan rashin yin aure.

Kara karanta wannan

Ana yawan yi mun gori da na ki yin aure amma na san Allah bai manta da ni ba - Fati Slow

A wata hira da sashin Hausa na BBC ta yi da ita a shirin 'Daga bakin mai ita', Fati ta ce aure lokaci ne kuma ta san Allah bai manta da ita ba.

Tsohuwar jarumar fim din ta ce aure nufi ne na Ubangiji don haka idan ya nufa za ta yi toh babu makawa za ta yi shi, sannan cewa idan Allah bai tsara zata yi aure ba a rayuwarta toh babu wanda ya isa ya daura mata shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel