Labarin Mary Ann: Hotunan Matar da ta fi kowa muni a duniya kuma ta ci gasar munana

Labarin Mary Ann: Hotunan Matar da ta fi kowa muni a duniya kuma ta ci gasar munana

  • Mary Ann Bevan mace ce da ta kafa tarihi a duniya inda ta ci gasar zama mace mafi muni a fadin duniya wacce aka yi a birnin London
  • Da farko ma'aikaciyar jinyar kyakyawa ce kuma ta yi aure inda ta haifa yara hudu, sai dai wata cuta kwatsam ta sameta inda muninta yasa aka koreta daga aiki
  • A wancan lokacin babu wanda ya san cutar, a cikin shekaru 5 kacal halittarta ta sauya kuma mijinta ya rasu, hakan yasa ta shiga gasar munana don taimakon yaranta

A wurin da kyan mutum ake ganinsa da matukar amfani, wannan matar mai suna Mary Ann Bevan ta bayyana kuma ta ci gasar munana inda aka nada ta macen da tafi kowa muni a duniya, lamarin da ya bata damar ciyar da iyalinta da makuden kudaden da ta samu.

Kara karanta wannan

Wata mata a Nasarawa: Dalilin da yasa na amince 'dan da na haifa ya dirka min ciki

Bayan wata muguwar cuta mai suna Acromegaly ta kama ta, kasusuwan fuskar Mary Ann Bevan sun ninka girmansu da kusan kashi uku, lamarin da ya sauya mata halitta baki daya.

Labarin Mary Ann: Hotunan Matar da ta fi kowa muni a duniya kuma ta ci gasar munana
Labarin Mary Ann: Hotunan Matar da ta fi kowa muni a duniya kuma ta ci gasar munana. Hoto daga telenganatoday.com
Asali: UGC

Labarin Mary Ann

An haifeta a Newham da ke London a shekarar 1874 kuma ta yi rayuwarta kamar yadda kowacce budurwa ke yi. Bayan kammala karatunta, ta zama malamar jinya a shekarar 1894 kuma babu dadewa ta auri Thomas Bevan, wanda suka haifa yara hudu da shi.

Sai dai babu dadewa farin cikin da iyalan suka shiga ya gushe sakamakon wata irin cuta da ta samu Mary mai suna acromegaly wacce a wancan lokacin likitoci ba su taba saninta ba, Telanganatoday ta ruwaito.

Labarin Mary Ann: Hotunan Matar da ta fi kowa muni a duniya kuma ta ci gasar munana
Labarin Mary Ann: Hotunan Matar da ta fi kowa muni a duniya kuma ta ci gasar munana. Hoto daga telenganatoday.com
Asali: UGC

Bayan shekaru kadan, Mary Ann ta yi fama da sauyi a jikinta wanda yake a bayyane sakamakon muguwar cutar. A cikin shekaru biyar, ba a iya gane ta kuma ta sauya daga kyakkyawar macen da aka santa inda ta koma mummuna.

Kara karanta wannan

Mutane su gama aibatani a zo ranar lahira su ga na shige Aljanna na barsu - Umma Shehu

Wannan ciwon yasa ake gudunta kuma aka kore ta daga wurin aikinta bayan mutuwar mijinta, lamarin da yasa iyalinta suka fada cikin mawuyacin hali.

A yayin da matsalarsu ta rashin kudi ta tsananta, Mary Ann ta yanke hukuncin yin sadaukarwa duk da zunde da tsokana da ta san za ta fuskanta.

A cikin shekarun 1920s, cike da burin samun kyautar kudi domin taimakawa 'ya'yanta, Mary Ann ta shiga gasar macen da tafi kowa muni a duniya inda ta samu nasarar lashe gasar.

Mary Ann ta yi watsi da darajarta duk saboda iyalanta, hakan ne yasa ta ci gasar kuma daga nan aka dinga bayyanata a matsayin macen da tafi kowa muni a duniya.

Indiatoday ta ruwaito cewa, sai dai tozarcin da ta fuskanta bai tsayar da ita ba inda ta dinga aiki a matsayin mummuna har zuwa mutuwarta a shekarar 1933.

Asali: Legit.ng

Online view pixel