'Yar Najeriya Mai Al’aurar Maza Da Mata Ta Samu Mijin Aure Bayan Labarin Ta Ya Bazu A Kafafen Sada Zumunta

'Yar Najeriya Mai Al’aurar Maza Da Mata Ta Samu Mijin Aure Bayan Labarin Ta Ya Bazu A Kafafen Sada Zumunta

  • Labarin wata ‘yar Najeriya mai suna Mystique Evolving ya yadu akan yadda aka haife ta da al’aurar namiji da ta mace
  • Bayan shekaru uku, ba masoyi kadai ta hadu da shi ba, har mijin aure ta samu don yanzu haka ta mike kafa a gidan shi
  • Matar ta bayyana yadda mutane da dama suka dinga surutai akan yadda Ubangiji ya halicce namiji da mace duk a jikin mutum daya

Wata ‘yar Najeriya mai suna Mystique Evolving ta yi bayani koma-bayan yadda mutane suka yarda da cewa Ubangiji maza da mata kadai ya halitta, inda tace ya halicci mata-maza.

An haifi matar da al’aurar namiji da ta mace. Labarin Mystique Evolving ya yadu a 2019 bayan BBC News Pidgin ta yi hira da ita inda ta bayyana kalubalen da take fuskanta a matsayin ta na mata-maza.

Kara karanta wannan

Magana ta dawo baya: Gwamnati ta ce babu kudin da malaman jami'a masu yajin-aiki ke nema

'Yar Najeriya Mai Al’aurar Maza Da Mata Ta Samu Mijin Aure Bayan Labarin Ta Ya Bazu A Kafafen Sada Zumunta
'Yar Najeriya Da Aka Haifa Da Al'aurar Maza Da Mata Ta Samu Mijin Aure Bayan Labarin Ta Ya Bazu A Kafafen Sada Zumunta. Hoto: @bbcnewspidgin
Asali: Instagram

A tattaunawar, matar cike da hawaye ta bayyana yadda ‘yan uwa da sauran jama’a suke kyamatar ta, wanda hakan ya sa take rayuwa a kebance fiye da shekaru 10 da suka gabata.

Mystique ta bayyana yadda ‘yan uwanta suka taba zane ta akan halin da take ciki.

Ta hadu da masoyinta na gaskiya

Bayan shekaru 3 da labarin ta ya yi ta yawo, ba masoyi kadai ta hadu da shi ba, har mijin aure ta samu sannan ‘yan uwanta sun dawo gare ta inda ta yi aure a shekarar 2021.

Bayan rungumar halin da take ciki da hannu bibbiyu, matar ta bayyana yadda take alfahari da yadda Ubangiji ya halicce ta a mata-maza.

Yanzu haka ita ce shugaban kungiyar lafiya ta Dynamic Initiative da kuma kare hakkin bil’adama, kungiyar da ke wayar da kai akan jinsi.

Kara karanta wannan

An gano sabon salon da Boko Haram suka dauka tun da dakarun Sojoji sun ci karfinsu

A tattaunawar da BBC News Pidgin ta yi da ita kwanannan, Mystique ta ce halin da ta shiga a matsayin ta na mata-maza ya nuna mata cewa mutum zai iya samun masoyin shi duk halin da yake ciki.

Ta koka akan yadda ake nuna wa mata-maza rashin tausayi a Najeriya inda tace akwai masu irin halittar ta a kasar nan.

Tsokacin ‘yan Najeriya

‘Yan Najeriya sun dinga bayyana ra’ayinsu dangane da mata-maza.

@y.c.s.i_heirs ta ce:

“Na dade ina ganin yadda yara mata-maza suke girma. A lokacin iyaye su kan rasa kayan da zasu sanya musu, na maza ko kuma na mata. Sai yaro ya rasa inda zai sa kan sa.
“Kawai a dinga kyautata musu saboda ba a san yadda mutum yake ji a jikin sa ba.”

@_8_beth ya ce:

“Mutum boye kansa zai dinga yi amma mutane irin su Bobrisky sun nuna musu yadda zasu yi rayuwar su. Na ji dadin yadda suke rayuwar su cike da nishadi.”

Kara karanta wannan

Rabo a kan rabo: Baiwar Allah ta haifi yara biyu a lokaci daya, kuma ba tagawaye ba ne

@nikkyay ya ce:

“A Amurka, yara 1500 duk mata-maza ne, don haka mutane 219,000 suna ta rayuwa a haka. Ina ganin a Najeriya ma akwai irin wannan yawan amma saboda kunya da addini sai su dinga boyewa.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel