Fostan Ali Jita na takarar kujerar gwamnan Kano ya fara yawo a shafin soshiyal midiya

Fostan Ali Jita na takarar kujerar gwamnan Kano ya fara yawo a shafin soshiyal midiya

  • Gabannin zaben 2023, fostan yakin neman zaben shahararren mawakin nan na aure da Kannywood, Ali Isa Jita, ya bayyana a shafin soshiyal midiya
  • An gano fostan ne a shafin abokiyar sana'arsa, Rahama Sadau, na soshiyal midiya
  • Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu inda wasu suka nemi a baiwa matasa damar nuna iyawarsu

Kano - Yayin da jama'a ke ci gaba da hasashen yadda babban zaben kasar na 2023 zai kasance, an gano wani fostan yakin neman zabe na shahararren mawakin nan na masana'antar shirya fina-finai na Kannywood, Ali Isa Jita.

Fostan wanda abokiyar sana'arsa Rahama Sadau ta wallafa a shafinta na Instagram, ya nuna cewa mawakin zai fito takarar kujerar gwamnan jihar Kano ne a zaben na 2023.

Kara karanta wannan

Atiku, Kwankwaso, da mutane 10 da za su iya bayyana niyyar tsayawa takara bayan Tinubu

Fostan Ali Jita na takarar kujerar gwamnan Kano ya fara yawo a shafin soshiyal midiya
Fostan Ali Jita na takarar kujerar gwamnan Kano ya fara yawo a shafin soshiyal midiya Hoto: rahamasadau
Asali: UGC

Sai dai kuma babu suna ko tambarin wata jam'iyyar siyasa a cikin hoton wanda ke dauke da rubutu kamar haka 'hangen nesa, sha'awa, aiki Jita 2023, Ali Isa Jita don neman gwamna, jihar Kano, Insha Allah'.

Jarumar ta kuma wallafa fostan dauke da rubutu da tayi kamar haka:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ehem Ehem . . . ‍♂️ Abu A GidanMu . . . @alijita1 ‍♂️"

Ali Jita ya yi martani

Jita ya yi mata martani a wajen sharhi inda ya ce za su maido da jarumar wacce take yar asalin Jihar Kaduna zuwa Kano.

Ya ce:

"Zamu dawo dake kano "

Martanin jama'a kan fostan

Tuni dai mabiya shafin nata suka yi martani a kan wannan hoto da ta wallafa inda Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikinsu a kasa:

kamal_a_zango ya yi martani:

Kara karanta wannan

Matan Arewa sun bayyana sunan gwamnan da suke kaunar ya gaji Buhari a zaben 2023

" #alijita1 gida gida kenanw"

abdultym ya rubuta:

"Wannan ci gaban abu ne mai kyau amma yaya cancantarsa? Me ya sani game da shugabanci don gudun maimaita abubuwan wadannan yan siyasa koma mafi muni wanda bama fatan haka. Idan har wannan gaskiya ne akwai bukatar ayi hira da shi don nuna kwarewarsa."

abdoul_jay ya ce:

"Har kar ba daudanci bace fah"

dbsakeena ya ce:

"Kano tamasa kadam"

realshittufatimah ta yi martani:

"Idan wannan gaskiya ne hakan na nufin Najeriya za ta je fiye da tunaninmua bari matasa su karbi mulki."

Mutane na son ganin ƙarshen mu da taurin bashi, Jarumar Kannywood ta koka

A gefe guda, mafi yawan jarumai mata a masana'antar shirya fina-finan Hausa, Kannywood, na shiga harkokin kasuwanci lokacin da zaren su ke ja a harkar fim da bayan sun ja baya.

Jaruma Sadiya Kabala, ta shaida wa BBC Hausa a wata hira cewa, jarumai mata na rungumar sana'a ne domin tsira da mutuncin su ko da bayan sun bar harkan fim.

Kara karanta wannan

Yari, Modu Sheriff, Al-Makura da jerin mutum 10 masu harin shugabancin APC a zaben 2022

Jaruma Sadiya na ɗaya daga cikin jarumai mata a Kannywood da suka fice daga harkar fim, kuma suka koma kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel