Atiku, Kwankwaso, da mutane 10 da za su iya bayyana niyyar tsayawa takara bayan Tinubu

Atiku, Kwankwaso, da mutane 10 da za su iya bayyana niyyar tsayawa takara bayan Tinubu

  • FCT, Abuja - A ranar 10 ga watan Junairun 2022 ne Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya tabbatarwa Duniya cewa zai nemi kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa
  • Legit.ng Hausa ta tattaro jerin wasu daga cikin ‘yan siyasan da ake zargin babu mamaki nan ba da dadewa ba, za su iya bayyana makamancin shirinsu na 2023
  • Daga cikin wadanda ake ganin su na harin zama shugaban Najeriya a zaben 2023 akwai kusoshi a jam’iyyar APC mai mulki da kuma wasu fitattun ‘yan adawa

Su wanene wadannan?

1. Atiku Abubakar

Wani rahoto da muka samu daga Jaridar Vanguard ya bayyana cewa ana sa ran Atiku Abubakar ya fito fili ya bayyana niyyarsa daga yanzu zuwa Afrilu.

2. Rabiu Kwankwaso

Wani babban ‘dan siyasa da alamu suke nuna zai nemi kujerar shugaban kasa a zaben 2023 shi ne tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu: Ba abin da zai hana ni zama shugaban kasa a zaben 2023 sai abu daya

3. Aminu Tambuwal

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal yana cikin wadanda suka nemi tikitin PDP a 2019, kuma da alamun zai sake jarraba sa’arsa a zabe mai zuwa.

4. Bala Mohammed

Tun kafin ya kammala wa’adin farko, an fara rade-radin Gwamnan Bauchi zai yi takarar shugaban kasa, har an ji wani Gwamna yana cewa ya cancanta.

5. Yahaya Bello

A jam’iyyar APC akwai wadanda za su nemi su gwabza da Bola Tinubu. Daga cikin wadanda suka fito karara su ne gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello.

Bola Tinubu
Osinbajo, Tinubu da Fayemi a gefe Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Facebook

6. Kayode Fayemi

Alamu su na nuna cewa akwai yiwuwar Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya nemi tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.

7. Dele Momodu

A rahoton da Legit.ng ta fitar, Dele Momodu yana cikin wannan sahu, kuma tuni har ya bayyana kudirinsa na fitowa takarar kujerar shugaban kasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Jonathan ya gamu da sarkakiya a titin 2023, Jiga-jigan APC ba su gamsu da sauya-shekarsa ba

8. Doyin Okupe

Dr. Doyin Okupe wanda ya yi aiki da shugabannin kasa biyu a Najeriya, ya fito tun kwanakin baya ya bayyanawa ‘yan kasar nan shirinsa na zama shugabansu.

9. Bukola Saraki

A karshen 2021 aka ji cewa Dr. Bukola Saraki ya shaidawa gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom cewa yana da burin sake tsayawa takarar shugaban kasa.

10. Anyim Pius Anyim

A baya an ji cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Sanata Anyim Pius Anyim ya dage kan batun neman takarar kujerar shugaban kasa har ya fara shiri.

11. Chris Ngige

Ku na da labari cewa wasu 'ya ‘yan jam'iyyar APC na reshen jihar Anambra sun bukaci Ministan kwadago, Chris Ngige ya nemi takarar shugaban kasa a 2023.

12. Goodluck Jonathan

Na karshe a jerin na mu shi ne tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda ake ta rade-radin cewa zai sauya-sheka zuwa APC, kuma a ba shi tutar takara.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin sanatoci 13 a Najeriya da ke neman kujerar gwamna a jihohinsu

Asali: Legit.ng

Online view pixel