Yari, Modu Sheriff, Al-Makura da jerin mutum 10 masu harin shugabancin APC a zaben 2022

Yari, Modu Sheriff, Al-Makura da jerin mutum 10 masu harin shugabancin APC a zaben 2022

  • A watan gobe na Fubrairun shekarar 2022 ne ake sa ran cewa jam’iyyar APC mai mulki za ta kira babban taronta, inda za ta zabi shugabannin kasa
  • Idanun kowa ya na kan wanda zai zama shugaban jam’iyya na kasa, idan har ta tabbata cewa zaben zai kankama, kuma a wannan lokaci da aka sa
  • Legit.ng Hausa ta tattaro jerin wasu daga cikin wadanda ake tunani za su nemi wannan mukami, a ciki har da ‘Dan shekara 36 da 'Yan majalisa

1. Abdulaziz Abubakar Yari

Tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari ya na cikin wadanda ke neman wannan kujera. Yanzu haka tsohon shugaban gwamnonin kasar bai rike da wani mukami tun da kotu ta ruguza nasarar da ya samu a zaben 2019, ta hana shi zuwa majalisa.

2. Ali Modu Sheriff

Sanata Ali Modu Sheriff wanda ya yi gwamna tsakanin 2003 da 2011 a jihar Borno ya na harin wannan kujera. Ali Modu Sheriff ya dawo jam’iyyar APC ne bayan ya shiga PDP har ya zama shugabanta na kasa, amma wa’adinsa ya kare da rikici.

Kara karanta wannan

Doyin Salami: Abubuwa 12 da ya dace a sani game da masanin da zai ceto tattalin Najeriya

3. Isa Yuguda

Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda ya shigo jam’iyyar APC, ya yi watsi da GPN. Ana tunanin Yuguda wanda ya taba rike Minista a gwamnatin Obasanjo ya na sha’awar wannan kujera, shi ma ya na zaune ne babu mukami tun 2015.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

4. George Akume

Ministan ayyuka na musamman da harkokin cikin gwamnati, George Akume yana cikin wadanda ake ganin za su yi takarar zama shugaban jam’iyyar APC na kasa. Akume ya yi shekara takwas a majalisar dattawa bayan ya yi gwamnan Benuwai.

5. Salihu Mustapha

A cikin masu neman wannan kujera da gaske akwai Alhaji Salihu Mustapha. Wannan ‘dan siyasa ya taba zama mataimakin shugaban jam’iyyar CPC na kasa. CPC na cikin jam’iyyun da suka dunkule aka kafa APC, ya dade tare da Muhammadu Buhari.

Shugabancin APC
Shugabannin APC da Buhari Hoto: nnn.ng
Asali: UGC

6. Mohammed Sani Musa

Kara karanta wannan

Dawo-dawo: Tsohon Shugaban kasa Jonathan ya yi zaman sirri da masu so ya koma kan mulki

Bisa dukkan alamu, Sanata mai wakiltar jihar Neja ta gabas, Mohammed Sani Musa zai nemi wannan kujera a zaben da za ayi. Mohammed Sani Musa ya fito ya shaidawa Duniya burinsa, ya na mai alwashin kawo gyara idan ya karbi shugabancin APC.

7. Tanko Al Makura

Wani Sanata da ke cikin jerin na mu shi ne Tanko Al Makura mai wakiltar Nasarawa ta kudu a majalisar dattawa. Tsohon gwamnan ya fito ne daga tsagin CPC kamar - Salihu Mustapha, kuma ana tunanin gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule na tare da shi.

8. Sunny Moniedafe

Tun tuni aka ji Sunny Sylvester Moniedafe ya fito ya na sha’awar zama shugaban APC na kasa. Jigon na jam’iyyar a Adamawa yace idan ya karbi ragamar, zai yi kokarin ganin an yi aiki da doka da tsari, kuma a samar da hadin-kai tsakanin jam’iyya da masu mulki.

9. Mohammed Saidu Etsu

A bara aka ji Mohammed Saidu Etsu mai shekara 36 a Duniya zai shiga takarar neman wannan kujera. Hadimin na gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya na sa ran matasan da ke ciin jam’iyyar APC za su taimaka wajen ganin burin na sa ya cika a zaben da za ayi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Gombe ya yi sabbin nade-nade a gwamnatinsa, ya nada sabon Babban Alkali

10. Mai Mala Buni

Duk a je a dawo, akwai yiwuwar ba za a yi wannan zabe a lokacin da aka tsara ba. Hakan zai iya bada dama gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya cigaba da zama a matsayin shugaban rikon kwarya, har zuwa lokacin da aka tsaida sababbin shugabanni na kasa.

Jonathan zai dawo?

A makonnin da suka gabata ne tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya hadu da masu yi masa fafutuka domin ganin ya sake neman mulkin Najeriya a 2023.

Dr. Goodluck Jonathan ya sa labule da wadannan mutane a wani otel a jihar Bayelsa. Bayan nan ne sai aka ga Jonathan tare da Buhari sun yi wani zama a Aso Villa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel