Bidiyon yadda wata jarumar Kannywood ta yi wa Daso ta-tas akan rawar TikTok

Bidiyon yadda wata jarumar Kannywood ta yi wa Daso ta-tas akan rawar TikTok

  • Wata jarumar Kannywood ta bayyana a wani bidiyo wanda shafin NaijaFamily na Facebook su ka wallafa inda ta yi wa Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso wankin babban bargo
  • Kamar yadda jarumar wacce ba ta shahara ba, ta bayyana abinda ya ke ranta cike da takaici, ta ce ba mutuncin Daso ba ne rawar da ta ke kwasa a shafin ta na TikTok
  • Jarumar ta kara da cewa, ya kamata manyan Kannywood su tsawatar wa Daso, ta kuma yi nuni da wani bidiyon ta wanda ta ke sanye da bakaken riga da wando ta na rawa daga zaune

Wata jarumar Kannywood ta fito fili ta fadi abinda ya ke damun ta dangane da Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso a wani bidiyo da NaijaFamily su ka wallafa a shafin su na Facebook.

Kara karanta wannan

Soyayya dadi: Yadda gimbiya ta bar masarauta da makudan miliyoyi ta auri talaka tukuf

Jarumar wacce ba ta shahara kwarai ba ta bayyana takaicin ta da alhini akan yadda Daso ta ke kwasar rawa a shafin ta na TikTok inda ta ce ya kamata manyan Kannywood su fada ma ta gaskiya.

Bidiyon yadda wata jarumar Kannywood ta yi wa Daso ta-tas akan rawar TikTok
Wata jarumar Kannywood ta yi wa Daso ta-tas akan rawar TikTok. Hoto: NaijaFamily
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar ta, Daso ta na zubar da mutuncin yaran ta, jikokin ta, zuri’ar ta da kuma su ‘yan Kannywood don haka ya kamata ta gyara.

Kamar yadda jarumar ta ce a farkon bidiyon:

“Don Allah manyan Kannywood ku na nan? Ku na nan da ran ku da lafiyar ku ku na ganin abinda baiwar Allar nan ta ke yi? Ku na ganin tabargazar da ta ke yi wa mutane a TikTok?
“Sai mu kananan yara ma su jini a jiki?, ko mu wallahi idan ance in yi abinda ta ke yi bazan iya ba. Juma’a guda ke ba ki yi happy Juma’a na karatu ba, ba ki yi na addu’a ba ki sa riga da wando ki dinga yi wa mutane rawa a TikTok?

Kara karanta wannan

Mata ga kotu: Mahaifiyar miji na ta umurci in saka guba a abincin jikokinta su mutu

“Ta yi a falo, ta yi a location, ta yi a titi, ta yi a gida? Shi ke nan duk Kannywood an rasa wanda zai tsawatar ma ta?”

Ta ce a cire tsoro a yi wa Daso magana

Ta ci gaba da cewa ya kamata ace an cire tsoro an fada ma ta gaskiya don ba wannan ne karon ta na farko da ta ke kwasar rawar ba a duba shafin ta, ta na rawar yadda ta ga dama.

Ta ce idan Daso ba ta kare mutuncin ‘yan Kannywood ba, ya kamata ta kare darajar yaranta da kuma jikoki da ‘yan uwa.

A karshen bidiyon an san ya bidiyon da Daso ta ke sanye da bakaken riga da wando zaune a kujera ta na kwasar rawar wakar Dj AB ta ‘Dan Lukuti’ ta na jefa hannu tare da juya jikin ta.

Hotunan bikin: An shafa Fatihar Saurayi da budurwan da suka hadu a Twitter

Kara karanta wannan

Na sha 'zagi' bayan na mayar wa fasinja N100,000 da ya yi mantuwa, Ayuba mai Napep

A wani labarin, wasu masoya Ameenu da Yetunde, sun bayyana wa mutane yadda su ka hadu har soyayyar su ta kai su ga aure a kafar sada zumuntar zamani.

Kamar yadda Ameenu ya wallafa wani hoto bisa ruwayar Legit.ng, inda ya nuna yadda hirar su ta kasance bayan lokacin da ya tura wa Yetunde sako a 2018.

Ameenu ya bayyana yadda ya fara ne da gabatar wa da Yetunde kan sa bayan ya tambayi yadda take.

Asali: Legit.ng

Online view pixel