Soyayya dadi: Yadda gimbiya ta bar masarauta da makudan miliyoyi ta auri talaka tukuf

Soyayya dadi: Yadda gimbiya ta bar masarauta da makudan miliyoyi ta auri talaka tukuf

  • Gimbiya Mako ta Japan da masoyinta Kei Komuro sun yi aure a hukumance ba tare da wata matsala ba
  • Bikin auren dai ya kasance cikar shekaru takwas da suka yi tare game da suka daga jama’a da kafafen yada labarai
  • Dangane da rasa matsayinta na sarauta, Mako ta yi watsi da kudin da za a ba ta na fam miliyan 1 (KSh 153) a matsayin gado

Gimbiya Mako ta kasar Japan ta fice daga gidan sarauta kuma ta auri saurayinta talaka mai suna Kei Komuro, inda ta bar kambunta na sarauta saboda soyayya.

Matashiyar mai shekaru 30 ta yi tattaki tare da masoyinta da suka hadu a jami'a a Tokyo ranar Talata, wanda ya kawo karshen zaman da suka yi na tsawon shekaru takwas zuwa zaman aure.

An tilastawa Mako barin kambun sarautarta kamar yadda al'adun Japan suka tsara game da auren talakawa.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Kwankwaso ya bayyana ra'ayinsa kan tafiya da Shekaru a siyasa

Soyayya dadi: Yadda gimbiya ta bar masarauta da makudan miliyoyi ta auri talaka tukuf
Gimbiyar Japan da ta saurayin da ta aura | Hoto: japantimes.com
Asali: UGC

Ta kuma hakura da karbar fam miliyan 1 (N565,884,695) wanda tun farko ta cancanci ta karba a matsayin ta na mai barin gado.

Duk dai saboda soyayya

A karon farko a rayuwarta, tsohuwar gimbiyar a yanzu za ta sauya suna daga Gimbiya Akishino zuwa Mako Komuro kawai.

Duk da cewa bikin ba shi da wata kima da daukaka, ya samu halartar iyayenta yarima Akishino, Gimbiya Kiko, da ‘yar uwarta Gimbiya Kako.

Amarya ta fitar da wata sanarwa bayan daurin auren da ke nuna cewa ta na ba da hakuri kan duk wata damuwa da shawarar da ta yanke ya haifar wa dangin.

Ta kuma soki kafafen yada labarai kan yada labaran karya game da mijinta, lamarin da ba wai kawai ya jawo mata bacin rai ba har ma ya taimaka wajen jefa ta da fama da matsalar rashin jin dadi a rai (PTSD).

Kara karanta wannan

Shugaban 'yan bindiga, Shehu Rekeb, ya sanar da dalilinsu na kai farmakin Goronyo

Daily Mail ta ruwaito cewa Mako da Kei sun shirya yin aure shekaru uku da suka gabata amma sun daga bikin zuwa gaba bayan wata badakalar kudi da ta shafi mahaifiyar Kei.

Yadda aka tsara tun faro

A baya mun kawo cewa, Aljazeera ta ruwaito za a daura auren gimbiya Mako ta kasar Japan da wani talaka mai suna Kei Komuro a watan Oktoba na 2021.

A baya kada, an lura cewa ma'auratan sun yi ta yawo a kafafen yanar gizo kwanaki da suka gabata bayan dangantakar su ta zama sananniya ga jama'a.

Domin ta auri mutumin da kowa yasan gama-gari ne kuma talaka, gimbiyar za ta ba da matsayin sarauta da gadon ta da ya kai biliyoyin kudade.

Asali: Legit.ng

Online view pixel