Mata ga kotu: Mahaifiyar miji na ta umurci in saka guba a abincin jikokinta su mutu

Mata ga kotu: Mahaifiyar miji na ta umurci in saka guba a abincin jikokinta su mutu

  • Christina Jacob ta sanar da wata kotu a Makurdi yadda uwar mijin ta ta umarci ta sa wa yaran mijin ta guba a abinci
  • Ta bayyana yadda sai bayan ta auri Obeya ta gano ya na da wasu yaran guda 4 daga mata daban-daban
  • Ta ce bayan ta tunkare shi ya nuna halin ko-in-kula, yayin da mahaifiyar sa ta bukaci ta sa ma yaran guba a abincin su

Makurdi - Christina Jacob ta sanar da babbar kotun da ke zama a Makurdi cewa mahaifiyar mijin ta ta umarci ta sa wa yaran mijin ta guba a abinci bisa ruwayar Daily Nigerian.

Jacob ta bukaci kotu ta raba auren ta da Linus Obeya har abada.

Mata ga kotu: Mahaifiyar miji na ta umurci in saka guba a abincin jikokinta su mutu
Mata ga kotu: Mahaifiyar miji na ta umurci in saka guba a abincin jikokinta. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Tsoro da zaman dardar: Yadda shirin NYSC ya zama abin tsaro ga 'yan bautar kasa

Kuma ta bukaci kotun ta ba ta damar rike yaran ta guda 2 kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Kamar yadda ta ce:

“Na hadu da Obeya a 2010 a Legas. Na samu ciki a 2013 daga nan miji na ya dakatar da auren, bisa al’adar mu ba a auren mace da ciki.
“Na jure duk wasu wahalhalu, yunwa da azaba daga mahaifiyar miji na da miji na da kan shi yayin da nake cikin auren."

Ta cigaba da cewa:

“Daga baya na gane cewa ya na da yara 4 daga wurin wasu matan daban-daban. Da na fuskance shi da maganar ya ce ni na sani.
“Bayan na sanar da mahaifiyar miji na ta ce in har zan iya zama da dan ta, in zuba wa yaran sa guba a abinci kawai.”

Jacob ta kara da rokon kotu ta taimaka ta kwato ma ta kwanuka, jannareto, kujeru, gado da kudin ta N150,000 da mijin ta ya ranta a wurin ta.

Kara karanta wannan

Wurin neman aiki, budurwa taci karo da wanda ta damfara N500,000 shekaru 5 da suka wuce, ya koya mata darasi

Ta kara da bukatar kotu ta umarci mijin ta da ya ci gaba da biya wa yaran ta kudin makaranta da sauran bukatu.

Ya ce ba ta bin shi ko sisi

A bangaren Obeya, ya amince da sakin kuma ya bukaci kotu ta ba shi damar rike yaran sa.

“Mata ta ba ta sanar da ni cewa ita bazawara ba ce har sai da na yi mata ciki a 2013.
“Ni nake yi mata girki da komai. Har yunkurin sa min guba ta dade ta na yi a lokuta daban-daban.
“Eh, ina da yara 4 daga mata 3. Sai dai daya ya rasu a 2018. Kuma babu wani yaro cikin su da ya taba zama tare da mu,” - Obeya

Ya musanta batun Jacob ta taba ranta ma sa ko sisi.

Alkalin kotun, Rose Iyorshe ta dage sauraron karar zuwa ranar 29 ga watan Oktoba don yanke hukunci.

A raba mu, ya ce na cika mugun ci, har rufe kicin yake yi da dare, Firdausi ta yi karar mijinta Haruna a kotu

Kara karanta wannan

Yana da hatsari: FG ta yi gagarumin gargadi ga 'yan Najeriya kan hada katin SIM da NIN

A wani labarin daban, a ranar Litinin wata Firdausi Sulaiman mai shekaru 23 ta maka mijin ta, Haruna Haruna a gaban kotun musulunci da ke zama a Magajin Gari a Kaduna tana bukatar a raba auren su da shi saboda yadda yake dukanta kamar gangar tashe sakamakon mungun cin abincin ta.

Kamar yadda NewsWireNGR ta bayyana, a korafin da ta yi wa Kotu, Firdausi wacce take zama a Rigasa da ke Kaduna ta ce har rufe kicin Haruna yake yi da dare.

Alkalin kotun, Nuhu Falalu, bayan sauraron bangarorin guda biyu, ya dage sauraron shari’ar har sai ranar 4 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel