Na sha 'zagi' bayan na mayar wa fasinja N100,000 da ya yi mantuwa, Ayuba mai Napep

Na sha 'zagi' bayan na mayar wa fasinja N100,000 da ya yi mantuwa, Ayuba mai Napep

  • Wani mai sana’ar Napep a Kaduna, Ayuba Yusuf, ya bayyana caccakar da ya fuskanta wurin jama’a saboda ya kudin fasinja da ya mayar
  • A cewar sa akwai mutanen da su ka dinga zagin sa su na ce masa ‘wawa’ saboda ya mayar wa fasinja N100,000 da ta manta a Napep din sa
  • Ya ce kudin da ba na shi ba ba sa ba shi sha’awa, kuma ko Napep din da ya ke ja ba ta shi bace, kawai rashin sa rai a na mutane ne

Kaduna - Wani mai Napep a Kaduna, Ayuba Yusuf, wanda ya mayar wa fasinja N100,000 ya bayyana irin mamakin da mutane su ka ba shi a ranar Litinin bisa ruwayar Daily Nigerian.

Yusuf, wanda ya na da diploma a Public Administration ya sanar da NAN yadda mutane kadan ne su ka yaba ma sa yayin da wasu su ka dinga caccakar sa saboda mayar da kudin da ya yi.

Kara karanta wannan

Mata ga kotu: Mahaifiyar miji na ta umurci in saka guba a abincin jikokinta su mutu

Na sha 'zagi' bayan na mayar wa fasinja N100,000 da ya yi mantuwa, Ayuba mai Napep
Na sha tsangwama bayan na mayar wa fasinja N100,000 da ya yi mantuwa, Ayuba mai Napep. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Daily Nigerian ta ruwaito yadda a bayanin sa ya ce ranar 19 ga watan Oktoba wata mata mai yara da misalin 6:45 na yamma ta tsayar da shi ana saura mintuna kadan 7pm ya yi, lokacin dakatar da masu napep daga yawo a titi.

Kamar yadda ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Na sanar da ita cewa na yi latti amma ta dinga roko na cewa daga tafiya ta dawo. Saboda tausayi na amince na yi sauri na ajiye ta don gudun karya dokar gwamnati.
“Saidai bayan isa ta gida na ga ta mantar da jakar ta a cikin Napep di na. Bayan na bude na ga kayan ta da kudi wadanda dama na yi niyyar ba zan taba ba.”

Yusuf mai shekaru 44 da yara 4 ya sanar da matar sa halin da ake ciki inda su ka kasa kunnuwan su a rediyo don jin cigiyar neman kudin.

Kara karanta wannan

Ba zan iya zama da matata ba, tamkar a wuta nake: Magidanci ya roki 'yan sanda su kai shi gidan yari

Daga baya matar sa ta ji an sanar da cigiyar a wani gidan rediyo wanda bayan hakan su ka mayar da komai har da kudin.

“Matar ta ji dadi kwarai inda ta cire N10,000 a cikin kudin wanda na ki amincewa amma ta matsa daga nan na amsa N4,000 sannan na ba wasu N6,000 a cikin gidan rediyon,” a cewar sa.

Napep din ma ba ta shi bace

Yusuf ya fara sana’ar Napep ne saboda karancin ayyuka bayan ya kammala makaranta. Ya kuma bayyana cewa Napep din ma ba ta shi bace, duk mako ya ke kai wa mai ita N15,000.

Ya ce mutane sun ba shi mamaki akan yadda su ka dinga caccakar sa saboda ya mayar da kudin da ba na shi bane.

Ya kara da cewa ya yarda da cewa duk abinda ba na shi bane ba na shi bane, a haka a ka dinga kiran sa ana sukar sa saboda ya mayar da kudin nan.

Kara karanta wannan

Tsoro da zaman dardar: Yadda shirin NYSC ya zama abin tsaro ga 'yan bautar kasa

Akwai wadanda su ka dinga mamaki inda su ke cewa ba su taba tunanin akwai mai Napep din da zai bar damar azurta kan sa da kan sa ba ta wuce shi.

Yayin tattaunawa da NAN, mai kudin, Maryam Umar ta ce ta ji dadin yadda ya mayar mata da komai, daga kudi har kayan ba tare da ya taba su ba.

“Na yi matukar farin ciki; ban taba sanin akwai irin mutane masu gaskiya irin sa ba. Ya na da rikon amana; dama mutane za su yi koyi da shi,” a cewar ta

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari.

A wani rahoton, wani matashi, Nsanzimana Elie ya kasance a baya ya na zama cikin daji saboda yanayin suffar sa, sannan mutanen kauyen sa har tonon sa su ke yi.

Akwai wadanda su ke kiran sa da biri, ashe daukaka ta na nan biye da shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wurin neman aiki, budurwa taci karo da wanda ta damfara N500,000 shekaru 5 da suka wuce, ya koya mata darasi

Mahaifiyar Elie ta ce Ubangiji ya amshi addu’ar ta na ba ta shi da ya yi bayan yaran ta 5 duk sun rasu, kuma ba ta kunyar nuna shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel