Koma bayan tattalin arziki laifin 'yan majalisa ne ba Buhari ba - MURIC

Koma bayan tattalin arziki laifin 'yan majalisa ne ba Buhari ba - MURIC

- Ƙungiyar MURIC ta yiwa tsohon shugaban ƙasa ƙarin haske dangane da wasiƙar da ya rubuta akan shugaba Buhari

- Ƙungiyar ta zargi 'yan majalisar tarayya da gurɓata tattalin arzikin ƙasar nan

Ƙungiyar 'yancin musulmai ta MURIC ( Muslim Rights Concern) ta bayyana cewa, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bai kasance abin zargi ba dangane da dubban matsalolin da suka shafi gurɓatar tattalin arzikin ƙasar nan ke fuskanta ba.

Shugaban ƙungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, shine ya bayyana hakan a wata sanarwar ranar Alhamis din da ta gabata, dangane da wasiƙar tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo da ya caccaki shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da cewar kar ya sake neman takarar shugabancin ƙasar nan a zaben 2019.

Shugaban ƙungiyar MURIC , Farfesa Ishaq Akintola
Shugaban ƙungiyar MURIC , Farfesa Ishaq Akintola

Farfesa Ishaq yake cewa, shugaban ƙasa Buhari bai cancanci wannan suka ba duba da cewar ko kaɗan shugaban ba ya da laifi wajen gurɓacewar tattalin arzikin ƙasar nan.

KARANTA KUMA: Makiyaya sun kai wani sabon hari jihar Binuwai

Ƙungiyar MURIC ta kuma yi imanin cewa, sukar Obasanjo za ta yi daidai da ace ya ɗora laifin akan 'yan majalisar tarayya domin kuwa sune ummul-aba-isin dake riƙe hannun shugaba Buhari wajen hana shi aikata alheri a ƙasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng