Amurka Ta Sa Kyautar Naira Biliyan 26 Tana Neman Gagarumin Sirrin Iran

Amurka Ta Sa Kyautar Naira Biliyan 26 Tana Neman Gagarumin Sirrin Iran

  • Amurka ta yi tayin bayar da kyautar dala miliyan 20 ga duk wanda ya ba da sahihan bayanai kan shirin nukiliyar kasar Iran
  • Gwamnatin Amurka ta kuma yi alkawarin yi wa masu bayar da bayanan muhimman wurare da kuma yiwuwar sauya musu matsuguni
  • Tayin na zuwa ne duk da ikirarin Donald Trump cewa hare-haren da aka kai wa cibiyoyin nukiliyar Iran sun lalata su gaba ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Gwamnatin Amurka ta sanar da bayar da kyautar har dala miliyan 20 ga duk wanda ya samar da bayanan sirri kan shirin nukiliyar Iran, duk da ikirarin Shugaba Donald Trump cewa an lalata cibiyoyin shirin gaba ɗaya.

Rundunar sojin Amurka ta bayyana cewa shirin Ma'aikatar Harkokin Wajen ƙasar mai suna Rewards for Justice ne zai bayar da kyautar tare da yiwuwar taimaka wa masu bayanan su sauya matsuguni.

Kara karanta wannan

Matashi ya dauki bindigogi da niyyar kashe Trump a Amurka

Shugaban kasar Amurka a wajen taro
Shugaba Donald Trump a wajen wani taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cewar sanarwar da Rundunar Sojin Amurka ta wallafa a shafinta na X, ana neman bayanai kan cibiyoyin nukiliyar Iran, kayan aikin da ake amfani da su da kuma mutanen da ke da alaƙa da shirin, ciki har da masana kimiyya.

Waɗanne bayanai Amurka ke nema?

Amurka ta buƙaci duk wanda ke da bayanai kan shirin nukiliyar Iran da ya ziyarci shafin intanet din ta domin miƙa bayanansa da neman kyautar.

Bayanan da ake nema sun haɗa da wuraren da ake gudanar da ayyukan nukiliya, kayan aikin da ake amfani da su da kuma mutanen da ke da hannu a shirin.

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ƙasashen duniya ke ci gaba da nuna damuwa kan ayyukan nukiliyar Iran, inda kyautar da za a bayar ta haura Naira biliyan 26.

Bayanai kan nukiliyar Iran

A shekarar 2025, Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ta bayyana cewa Iran na da sinadarin Uranium da ya kai kashi 60 cikin 100.

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta karɓi shaidu kan waɗanda ake zargi da yunkurin yi wa Tinubu juyin mulki

Wannan mataki ya kusa kaiwa kashi 90 cikin 100 da ake buƙata domin samar da makamin nukiliya, a cewar bayanan da aka fitar.

A watan Yunin 2025, Amurka da Isra'ila sun kai hare-hare kan wasu cibiyoyin nukiliyar Iran, inda suka nufi muhimman wuraren da ke da alaƙa da shirin ƙasar.

Mojtaba Khamenei
Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bayan hare-haren, Trump ya bayyana cewa an lalata cibiyoyin gaba ɗaya. Sai dai bincike da tantancewar da aka gudanar daga baya sun nuna cewa an raunana shirin ne, ba wai an kawar da shi gaba ɗaya ba.

An kama wanda zai kashe Trump

A wani labarin, mun ruwaito cewa jami'an hukumar tsaron fadar shugaban Amurka sun kama wani mutum kusa da fadar White House bisa zargin mallakar bindigogi da kuma barazanar kashe Shugaba Donald Trump.

Hukumar Tsaron Cikin Gida ta Amurka ta bayyana cewa jami'an sun ga Ronny Yordrix Guanipa Chrinos, ɗan ƙasar Venezuela, yana nuna halayen da suka zarge shi da aikata laifi a cikin wata mota da aka sace.

A cewar sanarwar hukumar, mutumin ya ce wasu muryoyi a kansa sun umarce shi da ya je Washington, D.C., domin kashe Trump. Jami'an sun kuma gano bindigogi a cikin motar, bayan da aka tabbatar cewa ta sata ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng