An ce Netanyahu zai Samu Matsala a Zaben Isra'ila yayin da ake Kirga Kuri'u
- Jam’iyyar Likud ta Benjamin Netanyahu ce ke kan gaba a sakamakon farko na zaɓen majalisar dokokin Isra’ila amma kuri'unta na raguwa
- Rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar Yashar ta Gadi Eisenkot ta zo ta biyu, yayin da jam’iyyun Larabawa suka koma matsayi na uku
- Wani manazarci ya ce Benjamin Netanyahu na iya fuskantar matsala wajen kafa gwamnati, lamarin da ka iya jawo sake gudanar da zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Isra’ila – Sakamakon farko na zaɓen majalisar dokokin Isra’ila ya nuna cewa jam’iyyar Likud ta Firaminista Benjamin Netanyahu ce ke kan gaba, duk da cewa ƙuri’un ta na raguwa.
Bayanai daga kwamitin zaɓe na ƙasar sun nuna cewa an ƙirga sama da ƙuri’u miliyan 2.1, inda Likud ta samu kashi 21.7 cikin 100 na sahihan ƙuri’un da aka ƙirga.

Source: Getty Images
Al Jazeera ta wallafa cewa sakamakon ya nuna cewa jam’iyyar Yashar ta jagoran ’yan adawa, Gadi Eisenkot, na ƙara samun ƙuri’u, yayin da jam’iyyun Larabawa suka samu matsayi na uku.
Ana fafatawa a zaben Isra'ila
A wani rahoto na farko da aka fitar, jam’iyyar Likud ta samu kashi 22.24 cikin 100 na ƙuri’un da aka ƙirga, amma bayan ƙarin ƙuri’u, adadin ya ragu zuwa kashi 21.7.
Jam’iyyar Yashar ta Eisenkot ta zo ta biyu da kashi 15.72 cikin 100, yayin da gamayyar jam’iyyun Larabawa ta zo ta uku da kashi 9.22.
Bayanai sun nuna cewa waɗannan sakamako na wucin gadi ne, kuma suna iya sauyawa yayin da ake ci gaba da ƙirga ƙuri’un.
Kimanin mutane miliyan 5.69 ne suka kada ƙuri’a daga cikin masu kaɗa ƙuri’a miliyan 7.33 da suka cancanta.
Eisenkot: 'Isra’ilawa na son sauyi'
Jagoran gamayyar ’yan adawa, Gadi Eisenkot, ya ce miliyoyin Isra’ilawa sun zaɓi sauyi saboda sun gaji da abin da ya kira ƙaryar Netanyahu.
A jawabinsa na farko bayan rufe rumfunan zaɓe, Eisenkot ya gargaɗi Netanyahu da kada ya yi amfani da batun tsaron Isra’ila domin cimma muradun siyasa.
Wata mamba a jam’iyyar Yashar, Orit Farkash-Hacohen, ta ce sakamakon zaɓen ya nuna cewa al’ummar Isra’ila ba sa son Netanyahu ya ci gaba da jagorantar ƙasar.
Ta yi iƙirarin cewa gamayyar jam’iyyun da ke goyon bayan Netanyahu ta yi babban rashin nasara, inda ta ce ya rasa kusan kujeru 20 kuma ba shi da rinjayen da zai ba shi damar kafa gwamnati.
AP ta wallafa cewa sai dai waɗannan kalamai na jam’iyyar Yashar ne, kuma sakamakon zaɓen bai kammala ba.

Source: Getty Images
Netanyahu na iya fuskantar matsala
Wani masanin siyasa, Dov Waxman, farfesa a Jami’ar California da ke Los Angeles, ya bayyana cewa Netanyahu na iya fuskantar matsala wajen kafa sabuwar gwamnati ko da kuwa jam’iyyarsa ce ta fi samun ƙuri’u.
A cewarsa, hasashen sakamakon ya nuna cewa jam’iyyun da ke adawa da gamayyar Netanyahu na iya samun kusan kujeru 68 a majalisar dokokin ƙasar.
Waxman ya ce mafi yawan masu zaɓe sun nuna cewa ba sa son Netanyahu ya ci gaba da zama firaminista, kuma ba sa son gamayyar gwamnatinsa ta ci gaba da mulki.

Kara karanta wannan
2027: Ana zargin wasu ƙusoshin APC sun fito da kudi don ruguza shirin hadewar yan adawa
Ya kuma bayyana cewa Netanyahu na iya ƙoƙarin nuna cewa jam’iyyun Larabawa ba su dace su zama abokan siyasa ba, domin hana Eisenkot samun goyon bayansu wajen kafa gwamnati.
A cewarsa, idan Eisenkot ya kasa kafa gwamnati, hakan na iya jawo sake gudanar da zaɓe, yayin da Netanyahu zai ci gaba da riƙe mukamin firaminista na rikon kwarya.
An yi zanga-zanga a Isra'ila
A wani labarin, kun ji cewa wasu ’yan Isra’ila sun gudanar da zanga-zanga suna neman gwamnati ta ɗauki alhakin gazawar tsaro.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaben kasar, inda Firaminista Benjamin Netanyahu zai fafata da 'yan adawa.
Yayin da ake shirin gudanar da zaben, shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi kira ga 'yan Isra'ila su goyi bayan Netanyahu.
Asali: Legit.ng

