Zaben Amurka: Musulma kuma bakar fata, Ilham Umar, ta lashe zabenta na 'yar majalisa

Zaben Amurka: Musulma kuma bakar fata, Ilham Umar, ta lashe zabenta na 'yar majalisa

- A karo na biyu, 'yar majalisa, Ilhan Omar, ta lallasa abokin hamayyarta

- Ilhan ta lashe sama da kashi 60 na kuri'un mazabarta dake jihar Minnesota

'Yar majalisar wakilai a Amurka, Ilhan Omar, ta sake lashe zabenta a matsayin mai wakiltan mazabar Minnesota ta 5, Minneapolis, a jihar Minnesota.

Ihlan, 'yar shekara 38 ta doke abokin hamayyarta na jam'iyyar Republican Lacy Johnson, wanda bakin fata ne kuma attajiri, da kashi 64.6% - 25.9% na kuri'u, Aljazeera ta ruwaito daga The Associated Press.

Ilhan Umar ce yar asalin kasar Somaliya ta farko da ta samu shiga majalisa kuma daya cikin mata musulmai biyu da aka fara zaba a tarihi a 2018.

Tana cikin kungiyar matasan mata 4 a majalisa; sune Rashida Tlaib daga Detroit, Alexandria Ocasio-Cortez daga New York City da Ayanna Pressley daga Boston.

Ta kasance babbar 'yar adawar Donald Trump kuma tana yawan caccakarsa da ma'aikatansa.

A watan Oktoba, Ilhan Omar ta caccaki Trump inda ta kira shi "mai nuna wariyar launin fata" saboda ya bayyana cewa ba 'yar Amurka bace.

KAI TSAYE: Sakamakon zaben kasar Amurka sun fara fitowa, Trump 213, Biden 238

Zaben Amurka: Musulma kuma bakar fata, Ilham Umar, ta lashe zabenta na 'yar majalisa
Ilhan Umar Credit: @AJEnglish
Asali: Twitter

Bayan da Joe Biden na jam'iyyar Democrat ya lashe zaben jiharta, Minnesota, Ilhan Umar ta sake tsokanan Donald Trump da hoto mai cewa "Kai babban mahaukaci ne".

KU KARANTA: Shugaba Trump ya na banbami, ya ce wasu sun yi zabe bayan lokaci ya kure

A wani labarin, Shugaba Donald Trump a ranar Laraba ya yi ikirarin cewa ya lashe zaben kujerar shugaban kasa, duk da cewa ba'a kammala fitar da sakamako ba, kamar yadda muka gano a bidiyon Aljazeera.

Hakazalika Trump ya lashi takobin garzayawa kotun koli domin dakatad da kirgan sauran kuri'u. "Mun lashe zaben," Trump yace a jawabin da yayi da safiyar Laraba a fadar White House.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng