Sabon tarihi: Ilhan Omar, Rashida Tlaib sun zama Musulmai na farko a majalisar wakilan Amurka

Sabon tarihi: Ilhan Omar, Rashida Tlaib sun zama Musulmai na farko a majalisar wakilan Amurka

- Ilhan Omar, 37, da kuma Rashida Tlaib, 42, suna kafa tarihi a siyasar kasar Amurka, inda suka zama mata Musulmai da suka lashe zabe a kujerun majalisar wakilan kasar Amurka

- Ilhan Omar, ta samu nasara a mazabar Minneapolis, inda ta doke Keith Ellison, wanda shima shine Musulmi na farko da aka zaba zuwa majalisar wakilan kasar

- Rashida Tlaib, ta samu nasara ne cikin sauki, kasancewar babu wanda ya tsaya takara daga jam'iyyar Republican a mazabar ta Detroit har zuwa Dearborn da ke cikin Michigan

A karon farko, wanda ya zama babban tarihi ga kasar Amurka, yadda labarin wasu mata musulmai guda biyu ya karade kafafen watsa labarai na duniya. Daya daga cikin matan, ta kasance yar gudun hijira daga yakin kasar Somalia, dayar kuwa ta kasance bakuwar haure daga kasar Palastine.

Wadannan mata guda biyu, a ranar Talatar nan, suna kafa tarihi a siyasar kasar Amurka, inda suka zama mata Musulmai da suka lashe zabe a kujerun majalisar wakilan kasar Amurka.

Gaba daya matan biyu, Ilhan Omar, 37, da kuma Rashida Tlaib, 42 -- sun fito ne daga jam'iyyar Democrat daga shiyyar Yamma, kuma sun kasance kamar masu yakin neman 'yancin jama'arsu da ke da karanci a shiyyar, da suka tsinci kawunansu a komar tsarin shugaban kasar Donald Trump na yaki da bakin haure.

KARANTA WANNAN: Kada ka jira sai gobe: Dawo da shafin Legit.ng akan manhajar Opera cikin hanyoyi ukku

Sabon tarihi: Ilhan Omar, Rashida Tlaib sun zama Musulmai na farko a majalisar wakilan Amurka
Sabon tarihi: Ilhan Omar, Rashida Tlaib sun zama Musulmai na farko a majalisar wakilan Amurka
Asali: Twitter

Ilhan Omar, ta samu nasarar lashe kujerar majalisar ne a mazabar Minneapolis, mazabar da jam'iyyar Democrats ke da karfi, inda ta samu nasara akan Keith Ellison, wanda shima shine Musulmi na farko da aka zaba zuwa majalisar wakilan kasar.

A bangarenta kuwa, Rashida Tlaib, ta samu nasara ne cikin sauki, kasancewar babu wanda ya tsaya takara da ita daga jam'iyyun hamayya a mazabar ta Detroit har zuwa Dearborn da ke cikin Michigan.

Labarinsu kusan na kamanceceniya da juna, kasancewar rayuwarsu da ta siyasarsu na tafiya ne akan shafin rayuwa daya.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Buhari ya amince da rahoton karin mafi karancin albashi zuwa N30,000

Ilhan Omar, Rashida Tlaib
Ilhan Omar, Rashida Tlaib
Asali: UGC

Wacece Ilhan Omar?

"Ni Musulma ce kuma bakar fata," a cewar Omar, cikin wata zantawa da ta yi da kamfanin wata mujalla.

"Na yanke shawarar tsayawa takara ne saboda ganin cewa ina da hanyoyi ko kuma wata baiwa ta wakilatar jama'ata, ta yadda kuma zan sama masu mafificin romon demokaradiya a wannan karnin siyasa da muke ciki," a cewarta.

Omar, na daga cikin wadanda suka tsallake rijiya ta baya baya a yakin da ya barke kasar Somalia,inda iyayenta suka yi hijira da ita zuwa wani sansanin 'yan gudun hijira ke da Kenya, a nan suka zauna tsawon shekaru hudu, daga bisani, iyayen suka sake yin wata hijirar zuwa kasar Amurka.

A 2016, ta samu nasarar lashe zaben kujerar majalisar wakilai ta tarayyar kasar, inda ta zama yar Somalia amma mazauniyar Amurka ta farko da ta fara zaman 'yar majalisar wakilai a kasar.

Wacece Rashida Tlaib?

Rashida Tlaib, bakuwar haure ce daga kasar Palastine, itace babba a cikin 'yaya 14 da iyayenta suka haifa. Yar gwagwarmaya ce, wacce ta zamarwa shugaban kasar Donald Trump ala-kai-kai a yakin zaben 2016 a mazabar Detroit, sai dai ta ce ba wai ta tsaya takara bane don kafa tarihi a matsayin Musulma.

"Na zabi yin takara ne duba da irin rashin adalcin da ake yi da kuma yarana, wadanda kullum suke tambaya ta game da addininsu (Musulunci) da kuma anin inda suka fito," a cewar Tlaib.

Kasancewar babu wani dan takara da ya fito daga jam'iyyar adawa ta Republican, wannan ne ya baiwa Tlaib nasarar lashe zaben da ya gudana a ranar Talatar cikin sauki.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel