Iran Ta Shirya Kaddamar da Makamin da Zai Girgiza Makiyanta

Iran Ta Shirya Kaddamar da Makamin da Zai Girgiza Makiyanta

  • Rundunar IRGC ta Iran ta ce tana shirin bayyana wani sabon makami da ta kira “Uban Dukkan Bama-bamai”
  • Rahotanni sun ce Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayar da umarnin shirya tsare-tsaren kai hari kan kayayyakin samar da makamashin Iran
  • Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce ƙasashe da dama na ci gaba da hulɗa da Iran duk da takunkumin da Amurka ta kakaba mata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Rundunar juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta ce tana shirin bayyana wani sabon makami da ta kira “Uban Dukkan Bama-bamai”.

Rundunar IRGC ta bayyana hakan ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takun-saka tsakanin Tehran da Washington.

Iran za ta kaddamar da makamai
Wasu makamai masu linzami na Iran Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa kamfanin dillancin labarai na Young Journalists Club na Iran ya rawaito kakakin rundunar, Hossein Mohebbi, ya bayyana hakan.

Kara karanta wannan

Rigima sabuwa: Sabon shirin da Amurka da Iran suka shirya kan Iran

Hossein Mohebbi ya bayyana cewa suna shirin bayyana makamin, wanda ya ce sabon abu ne ga abokan gabansu.

“Muna matakin shirye-shiryen bayyana ‘Uban Dukkan Bama-bamai’. Wannan wani sabon abu ne ga abokan gaba.” In ji shi.

Sai dai kakakin bai yi ƙarin bayani kan irin makamin ba, ko ƙarfin da yake da shi, ko lokacin da za a bayyana shi.

Amurka na shirin sake kai hari kan Iran

A wani rahoto daban, an bayyana cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayar da umarnin shirya tsare-tsaren kai hari kan kayayyakin samar da makamashin Iran, idan ya yanke shawarar sake fara hare-haren soji.

Rahoton ya danganta shirin da yiwuwar amfani da abin da ake kira “Uwar Dukkan Bama-bamai”, wato Mother of All Bombs (MOAB), wadda aka bayyana a matsayin bam mafi girma marar amfani da makamashin nukiliya a cikin makaman Amurka.

Sai dai bayanin bai tabbatar da cewa an yanke shawarar aiwatar da harin ba, ko kuma an yi amfani da bam ɗin.

Kara karanta wannan

Houthi ta zafafa hare hare kan Saudiyya, ta yi gagarumar barna

Kasashe na ci gaba da hulɗa da Iran

A wani ɓangaren, Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce ƙasashe daban-daban a duniya na ci gaba da hulɗa da Iran duk da takunkumin da Amurka ta kakaba mata.

Kamfanin dillancin labarai na Fars ya rawaito cewa Pezeshkian ya bayyana hakan ne yayin wani taro na bikin Ranar Fitar da Kayayyakin Iran zuwa Ƙasashen Waje.

Shugaban na Iran ya zargi Trump da yin barazanar ƙwace man fetur da iskar gas na ƙasar, yana mai cewa Iran ba za ta taɓa bari ya ƙwace albarkatun nata ba.

“Sun yi tunanin cewa ta hanyar kashe shugabanmu, za su iya wargaza ƙasar.” In ji shi.

Haka kuma, kalaman nasa na zuwa ne yayin da takunkumin Amurka da barazanar ɗaukar matakin soji ke ƙara tsananta dangantakar ƙasashen biyu.

Iran za ta bayyana sabon makami
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: @drpezeshkian
Source: Twitter

Iran ta musanta hannu a hare-haren Houthi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Iran ta nesanta ƙanta daga dukkan ikirarin da ake yi na cewa tana da hannu a samamen da 'yan ƙungiyar Houthi ke gudanarwa a ƙasar Yemen.

Magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baqaei, ya bayyana cewa rundunar sojin Yemen tana aiki ne bisa muradun kanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng