Zaben 2019: Tsohon shugaban kasar Amurka Bill Clinton zai gana da Buhari da Atiku

Zaben 2019: Tsohon shugaban kasar Amurka Bill Clinton zai gana da Buhari da Atiku

An sa ran tsohon shugaban kasar Amurka, Bill Clinton, zai kai ziyarar kwana daya zuwa Najeriya a ranar Juma’a, 15 ga watan Feburairu, kwana daya kafin gudanar da zaben shugaban kasar Najeriya, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yayin ziyarar, Clinton zai yi ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ke neman zarcewa a karkashin inuwar jam’iyyar APC, sa’annan zai goga gemu da gemu da babban abokin hamayyan Buhari, Atiku Abubakar daga jam’iyyar PDP.

KU KARANTA: Daga gidan yari, tsohon gwamna Dariye ya nemi yan Najeriya su zabi Buhari a 2019

Zaben 2019: Tsohon shugaban kasar Amurka Bill Clinton zai gana da Buhari da Atiku
Buhari, Atiku da Clinton
Asali: UGC

Sai dai majiyoyi daga farfajiyan ofisoshin jakadanci sun bayyana cewa Clinton ba zai kwana a Najeriya zuwa ranar zabenba, sun tabbatar da zai koma kasar Amurka a ranar, ma’ana ziyarar tasa ta yini guda ce.

Don haka ake sa ran isowar Clinton da sanyin safiyar Juma’a, 15 ga watan Feburairu kafin yan takarar shugaban kasar su wuce garuruwansu don shirin kada kuri’a, inda Buhari zai tafi Daura, yayin da Atiku zai nufi Adamawa.

Shima shugaban jam’iyyar PDP, Prince Uche Secondus ya tabbatar da wannan ziyara da Bill Clinton zai kawo Najeriya a ranar jajibarin zabe, inda yace tuni aka sanar dasu game da ziyarar wannan babban bako.

“Mun sane da zuwansa, bamu da wani abin boyewa, abinda muke kawai shine a gudanar da zaben gaskiya da adalci, kuma bamu bukatar katsalandan daga kowaye a cikin aikin hukumar zabe INEC da ma hukumomin tsaro.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel