Abin Tausayi: Jarirai da Aka Haifa 15 Sun Rasa Rayukansu bayan Gobara a Asibiti

Abin Tausayi: Jarirai da Aka Haifa 15 Sun Rasa Rayukansu bayan Gobara a Asibiti

  • Akalla jarirai 15 ne suka mutu bayan gobara ta tashi a sashen haihuwa na babban asibitin PIMS da ke Islamabad, Pakistan
  • Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne bayan fashewar na’urar sanyaya iska, inda jarirai 16 ke cikin ɗakin renon jarirai
  • Firayim minista Shehbaz Sharif ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa domin tantance musabbabin gobarar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Islamabad, Pakistan - Akalla jarirai 15 ne suka mutu bayan wata gobara ta tashi a sashen haihuwa na babban asibitin Pakistan.

Gobarar ta tashi ne da safiyar Laraba bayan wata na’urar sanyaya iska ta fashe a sashen kula da mata masu juna biyu na asibitin.

Jarirai 15 sun mutu a gobara a asibiti
Jami'an agajin gaggawa bayan tashin gobara a asibitin Pakistan da ya kashe jarirai. Hoto: Reuters.
Source: Getty Images

Yadda jariri daya ya tsira da rayuwarsa

A lokacin da lamarin ya faru, akwai jarirai 16 a ɗakin renon jarirai, amma an samu nasarar ceto jariri guda ɗaya kacal, kamar yadda jami’an asibitin suka bayyana, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya

Jami’an ceto sun ce an kashe gobarar, yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin sanyaya wurin domin tabbatar da cewa babu sauran barazana.

Ƙungiyoyin agajin gaggawa sun garzaya asibitin domin shawo kan gobarar, kwashe marasa lafiya da kuma tabbatar da tsaron yankin da lamarin ya shafa.

Ministan harkokin cikin gida, Mohsin Naqvi, da Firaminista Shehbaz Sharif sun bayyana alhininsu kan mummunan lamarin.

Sharif ya ce:

“Rasuwar yara wani babban rashi ne da ba za a iya maye gurbinsa ba."

Magajin garin Islamabad ya kafa wani kwamitin bincike mai ɗauke da hukumomi daban-daban, tare da umarnin gabatar da rahoto cikin sa’o’i 24, cewar Independent.

Kwamitin zai binciki musabbabin gobarar da yadda ta bazu, tare da tantance ko an samar da isassun matakan kariya daga gobara da kuma yadda aka gudanar da aikin ceto.

Iyaye sun shiga dimuwa bayan mutuwar jarirai 15
Motar daukar marasa lafiya a bakin asibitin da abin ya faru da wani mahaifi yana kuka bayan rasa jaririnsa. Hoto: Reuters, AFP.
Source: UGC

Abin da Shugaban Pakistan ya ce

Shugaban Pakistan, Asif Ali Zardari, shi ma ya jajanta wa iyalan wadanda suka rasu, yana mai bayyana mutuwar jariran a matsayin abin tayar da hankali da babban rashi.

Kara karanta wannan

Gwamna ya dauki zafi da yan bindiga suka kai mummunan hari masallaci ana cikin Sallah

Zardari ya bukaci a gano wadanda ke da alhakin faruwar lamarin tare da hukunta su bisa doka, sannan ya yi kira ga asibitoci su tabbatar da ingantattun matakan kariya daga gobara.

Ya kuma jaddada muhimmancin samar da tsare-tsaren gaggawa, musamman a sassan da ake kula da jarirai.

Wata mahaifiya ta shiga mummunan yanayi

Mohammad Sami, wacce ta haifi jaririnta kwanaki uku kafin faruwar lamarin, ta ce jaririnta yana karbar kulawa ta musamman a ɗakin renon jarirai lokacin da gobarar ta tashi.

Cikin kuka ta ce:

“Ban san abin da zan ce ko wanda zan zarga ba. Na rasa ɗana.”

Jami’an asibitin sun sanar da iyalan wadanda suka rasu cewa za a mika gawarwakin jariran bayan kammala dukkan takardun da suka dace.

Ministan lafiya, Syed Mustafa Kamal, ya shaida cewa yana tafiya daga Karachi zuwa Islamabad domin jagorantar binciken da kansa.

Bayan haihuwar jarirai 5, mata ta mutu

A baya, an ji cewa Hafsatu Yusuf, matar da aka ruwaito ta haifi 'yan biyar a asibitin Murtala dake birnin Kano ta rasu sakamakon zubar jini.

An gudanar da jana'izar marigayiyar a unguwar Hotoro yayin da jariranta biyar suke karkashin kulawar likitoci ta musamman a asibiti.

Ma'aikatar lafiya ta yi kira ga al'umma da su tallafa wa jariran da madara da tufafi don ci gaba da kula da su bayan rasuwar Hafsatu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.