Duk Mai Rai: 'Yan agaji 7 sun rasu a jihar Kano

Duk Mai Rai: 'Yan agaji 7 sun rasu a jihar Kano

Labarin da muke samu daga majiyar mu na nuni ne da cewa a yammacin jiya Lahadi ne Allah ya karbi Rayuwar wasu 'yan agaji bakwai daga cikin 'yan agajin na kungiyar nan ta addinin Musulunci ta JIBWIS da aka fi sani da suna Izala da suka fito daga karamar hukumar Kibiya ta jihar Kano.

Mun samu haka zalika cewa 'yan agajin sun rasu ne a sanadiyyara hadarin mota da sukayi akan hanyarsu ta mayar da yan uwan su 'yan agajin da sukazo wajen wani taron su a jihar ta Kano din daga bangaren garin Saya-Saya/ Kafin Dalawa/ Burum-Burum.

Duk Mai Rai: 'Yan agaji 7 sun rasu a jihar Kano
Duk Mai Rai: 'Yan agaji 7 sun rasu a jihar Kano

Legit.ng dai tana addu'ar Allai yayi masu gafarta ya kuma lullube su da Rahmar sa, Amin.

Haka ma dai mun samu cewa a daren Alhamis 28/12/2017 wasu mahara suka kaddamar da kisan gilla ga dan kasuwa Alhaji Sule Itas/Gadau da ake yi wa lakabi da Lauya.

Kafin rasuwar sa shine Manajan kamfanin Gerawa Global Construction Company Limited, babban kamfanin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bude yayin ziyarar jihar Kano. Maharan sun kashe shi ne a gidan sa dake unguwar Tokarawa a jihar Kano.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng