Jam’iyyun Larabawa Ta Fadi Wanda Za Ta Goyawa Baya tsakanin Netanyahu da Eisenkot

Jam’iyyun Larabawa Ta Fadi Wanda Za Ta Goyawa Baya tsakanin Netanyahu da Eisenkot

  • Babbar kungiyar jam’iyyun Larabawa a Isra’ila ta sanar da goyon bayanta ga Gadi Eisenkot domin ya kafa sabuwar gwamnati
  • Jam’iyyar United Torah Judaism ta ki marawa Benjamin Netanyahu baya, lamarin da ya kara raunana matsayinsa
  • Jam’iyyun sun samu kujeru 19 a zaben da aka gudanar, abin da ya kara musu muhimmanci wajen tantance wanda zai jagoranci Isra’ila

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Isra'ila - Babbar kungiyar jam’iyyun Larabawa a Isra’ila ta sanar da goyon bayanta ga tsohon babban hafsan sojin kasar, Gadi Eisenkot.

Jam'iyyun sun yi haka ne domin ya kafa sabuwar gwamnati bayan zaben majalisar dokokin kasar da aka gudanar a ranar 27 ga Oktoban 2026.

Jam'iyyar za su yi wa Netanyahu tsiya
Jagora a jam'iyyar Yashar, Gadi Eisenkot yana jawabi ga masoyansa a Tel Aviv da Firayim minista, Benjamin Netanyahu. Hoto: Jack GUEZ / AFP, Benjamin Netanyahu.
Source: Getty Images

Matakin ya zo ne a daidai lokacin da Firaminista Benjamin Netanyahu ke fuskantar kalubale wajen samun goyon bayan jam’iyyun da suka saba mara masa baya, musamman bayan jam’iyyar United Torah Judaism ta ki ba shi goyon baya, cewar France24.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya fito yana murna da rusa takarar Atiku da dukkan 'yan ADC a Najeriya

A ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamba, Shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, ya ci gaba da ganawa da wakilan jam’iyyun siyasa domin tattauna wanda zai samu damar kafa gwamnati.

Jam’iyyun Larabawa sun marawa Eisenkot baya

Kungiyar Joint List, wadda ta samu kujeru 11 a zaben, ta sanar da cewa za ta shaidawa Shugaba Herzog shawarar marawa Eisenkot baya domin ya kafa gwamnati.

A cikin sanarwarta, kungiyar ta ce za ta sanar da shugaban kasar cewa ta amince a bai wa Eisenkot damar kafa sabuwar gwamnati.

Ita ma jam’iyyar Raam, wadda ta samu kujeru takwas, ta bayyana goyon bayanta ga tsohon babban hafsan sojin.

Hakan ya sa jam’iyyun Larabawa suka samu jimillar kujeru 19 a sabon majalisar dokokin Isra’ila, wanda ya zama adadi mafi yawa da suka taba samu.

Netanyahu ya rasa goyon bayan jam’iyyar addini

A wani bangaren, jam’iyyar United Torah Judaism, wadda ta kasance cikin masu goyon bayan Netanyahu a zabuka biyar da suka gabata, ta sanar da cewa ba za ta ba shi shawarar kafa gwamnati a wannan karon ba.

Kara karanta wannan

Jiga jigan PDP 3 sun mutu a hatsarin mota a Kaduna yayin kamfen siyasa

Ofishin shugaban Isra’ila ya bayyana cewa jam’iyyar ta sanar da rashin amincewa da ba da shawarar kowane dan majalisa domin kafa gwamnati.

United Torah Judaism tana da kujeru bakwai a majalisar dokokin kasar mai mambobi 120.

Jam’iyyar da kuma Shas, wata kungiyar masu tsananin bin addinin Yahudanci, sun dade suna neman a ci gaba da ba daliban addini kebewar shiga aikin soja.

Sai dai Gadi Eisenkot ya sha bayyana cewa yana son kawo karshen wannan kebewa, lamarin da ya zama daya daga cikin manyan batutuwan da za su iya kawo sabani tsakaninsa da jam’iyyun addini.

Netanyahu ya rasa goyon bayan jam'iyyun Larabawa
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Yadda za a kafa sabuwar gwamnatin Isra’ila

Rahoton ya bayyana cewa Benjamin Netanyahu da kungiyoyin da ke tare da shi, ciki har da United Torah Judaism, suna da kujeru 53 a sabuwar majalisa.

A daya bangaren, bangaren Gadi Eisenkot yana da kujeru 48, yayin da jam’iyyun Larabawa suka samu kujeru 19.

Dokar kasar ta bai wa Shugaba Isaac Herzog damar zabar dan majalisar da zai ba wa damar kafa gwamnati, ko da yake al'adar siyasar kasar ita ce a bai wa wanda ya samu shawarar goyon bayan jam’iyyu mafi yawa.

Kara karanta wannan

2027: Kusoshin jam'iyyar NDC da aka rabu da su alhali Peter Obi yana tsakiyar kamfe

Ana binciken magudin zabe a Isra'ila

An ji cewa hukumar zaɓen Isra'ila ta ce binciken da ta gudanar bai gano wata shaida ta maguɗi ko rashin bin ƙa'ida a zaɓen da aka yi makon jiya ba.

Rahoton hukumar ya kawo cikas ga ƙoƙarin Firaminista Benjamin Netanyahu da magoya bayansa na nuna cewa an yi maguɗi a zaɓen.

Sakamakon zaɓen ya nuna cewa ƙungiyar jam'iyyun masu ra'ayin addini da kishin ƙasa ta Netanyahu ta rasa rinjayen kujeru a majalisar dokoki Read more:

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.