Mutanen Israila Sun Muzgunawa Falasdinawa, an Kona Masallatai da Gonaki

Mutanen Israila Sun Muzgunawa Falasdinawa, an Kona Masallatai da Gonaki

  • An zargi 'yan share wuri zauna da kona masallatai biyu da kuma motoci da gonaki a yankin Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye
  • Hare-haren sun zo ne kwana biyu bayan wani rikici tsakanin Isralawan da Falasɗinawa ya yi sanadiyyar mutuwar Falasɗinawa huɗu da Isra’ilawa biyu
  • Rikicin Isra'ilawa ya ƙara tsananta yanayin tsaro a yankin, yayin da hare-haren da ake kai wa Falasɗinawa ke ƙaruwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Birnin Tel-Aviv - Mahukuntan Falasɗinawa sun ce Isralawa 'yan share wuri zauna sun ƙona masallatai biyu tare da motoci da gonaki a Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye, yayin da tashin hankali ke ci gaba da ƙaruwa a yankin.

Sabbin hare-haren sun faru ne kwana biyu bayan wani rikici tsakanin 'yan share wuri zauna da Falasɗinawa kusa da ƙauyen Tal, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Falasɗinawa huɗu da Isra’ilawa biyu.

Kara karanta wannan

Amurka ta fadi abin da ta ke koya wa sojojin Najeriya a jihar Bauchi

An kona masallacin Falasdinawa
Masallacin Falasdinawa da wasu Israila suka kona Hoto: Hisham K.K. Abu Shaqra
Source: Getty Images

Tashar BBC ta kawo rahoton cewa bangarorin biyu sun zargi juna da haddasa tashin hankalin.

Rikicin ya ƙara dagula lamarin a Yammacin Kogin Jordan, inda hare-haren da masu tsattsauran ra’ayin ’yan share wuri zauna ke kai wa Falasɗinawa ke ƙaruwa, tare da ƙarfafawar wasu masu tsattsauran ra’ayi a cikin gwamnatin Isra’ila ta yanzu.

An kai hare-hare kan ƙauyuka biyu

Rahotannin Falasɗinawa sun ce an kai hari kan ƙauyuka biyu a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye cikin daren jiya, inda aka lalata motoci, aka sace kayayyaki sannan aka rubuta kalaman ƙiyayya a bangon gidaje.

Magajin garin Qusra ya ce ’yan share wuri zauna sun cinna wa wani masallaci da ake ginawa wuta.

Abdul Azim Wadi ya ce ’yan share wuri zaunan sun rubuta kalmar “ramuwa” a bangon masallacin.

Sojojin Isra’ila sun ce an tura dakarunta zuwa Qusra, yayin da ’yan sanda za su gudanar da bincike tare da tattara shaidu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya shawarci Yari game da nema wa Tinubu kuri'a a zaben 2027

Mahukuntan Falasɗinawa sun ce a wani lamari na daban, ’yan share wuri zauna sun ƙona wani masallaci a ƙauyen Kour tare da rubuta kalamai a bangonsa.

Tun bayan mummunan rikicin da ya faru a Tal ranar Juma’a, Falasɗinawa sun ce an kai hare-haren ’yan share wuri zauna da dama kan ƙauyuka a faɗin Yammacin Kogin Jordan.

Isra’ila ta kama Falasɗinawa da dama

Rundunar Tsaron Isra’ila (IDF) ta gudanar da samame tare da kama Falasɗinawa da dama a wani aikin da ta kira na “yaƙi da ta’addanci”.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya mayar da martani kan lamarin Tal ta hanyar yin alƙawarin ɗaukar “mataki mai ƙarfi”.

Hakan na iya haɗawa da rusa gidajen wasu Falasɗinawa biyu da ake zargi da hannu a lamarin.

A cikin ’yan watannin nan, an samu ƙaruwa sosai a hare-haren ’yan share wuri zauna na Isra’ila a Yammacin Kogin Jordan.

Hakan ya jawo Allah wadai daga ƙasashen duniya, amma har yanzu ba a ga wata alama mai ƙarfi ta kawo ƙarshen hare-haren ba.

Yahudawa sun kona masallacin Falasdinawa
Wani bangare na masallacin Falasdinawa da wasu Isra'ilawa suka kona Hoto: Hisham K K Abu Shaqra
Source: Getty Images

Rikici ya ƙaru tun bayan yakin Gaza

Yanayin ya riga ya fara tabarbarewa tun kafin hare-haren da Hamas ta jagoranta kan Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Kara karanta wannan

Ba tare da tsoro ba, Kwankwaso ya fadi rukunin mutane 2 da za su gwabza a zaben 2027

Sai dai tun bayan barkewar yakin da Isra’ila ke yi da Hamas a Gaza, tashin hankalin da ’yan share wuri zauna ke haddasawa a Yammacin Kogin Jordan ya ƙara tsananta.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce an kashe Falasɗinawa 1,114 a Yammacin Kogin Jordan, mafi yawansu daga hannun rundunar sojojin Isra’ila. Ta ce aƙalla 35 daga cikin waɗanda aka kashe sun mutu ne sakamakon hare-haren ’yan share wuri zauna.

Ta kuma ce an kashe Isra’ilawa 41, ciki har da fararen hula da jami’an tsaro, a hare-haren Falasɗinawa ko yayin ayyukan sojojin Isra’ila a Yammacin Kogin Jordan tun bayan fara yakin Gaza.

Israila na gina matsugunan jama'arta

Isra’ila ta gina ɗaruruwan matsugunai da ke ɗauke da Isra'ilawa 700,000 tun bayan da ta mamaye Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Kudus a lokacin yakin Gabas ta Tsakiya na 1967.

Falasɗinawa na son waɗannan yankuna, tare da Gaza, su kasance wani ɓangare na ƙasar da suke fatan kafawa a nan gaba. Kimanin Falasɗinawa miliyan 3.3 ne ke rayuwa tare da ’yan share wuri zauna.

A karkashin dokokin ƙasa da ƙasa, matsugunan ba halastattu ba ne domin sun sabawa doka.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ware malaman musulunci yana biyansu duk wata, ya fada masu irin wa'azin da za su yi

Israila ta kashe Falasdinawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa sojojin Isra'ila sun kai sababbin hare-haren sama a yankuna da dama na Zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar akalla Falasdinawa biyu.

Hare-haren sun lalata gidaje a sansanonin 'yan gudun hijira na Bureij da Jabalia da kuma unguwannin Zeitoun da Tal al-Hawa da ke birnin Gaza.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com