Bayan Sallar Juma'a, Girgizar Ƙasa Ta Faɗawa Iran ana tsaka da Musayar Wuta da Isra'ila
- Girgizar ƙasa mai karfin 5.2 ta faru a tsakiyar Iran yayin da ƙasar ke ci gaba da musayar wuta da Isra'ila tun makon da ya gabata
- Rahotanni sun nuna cewa duk da girgizar kasar ba ta zurfi a cikin ƙasa ba amma lamarin ya ƙara jefa jama'a a cikin fargaba
- Tun ranar Juma'a da ta gabata, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke fama da hare-hare daga Isra'ila, lamarin da ya ƙara dagula sha'anin taaro a Gabas ta Tsakiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Rahotanni daga Iran sun tabbatar da cewa an yi wata gagarumar girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 5.2 a tsakiyar ƙasar ranar Juma'a, 20 ga watan Yuni, 2025.
Wannan girgizar ƙasa dai na zuwa ne a daidai lokacin da jamhuriyar musulunci ta Iran ke musayar wuta tsakaninta da Isra'ila.

Asali: Getty Images
Shafin Exx Alert ya tabbatar da cewa an samu girgizar ƙasa a wani gajeren saƙo da ya wallafa a manhajar X wadda aka fi sani da Twitter a daren Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 5.2 ta faru a tsakiyar Iran," in ji sanarwar.
Wace irin girgizar ƙasa aka yi a Iran?
Rahotanni sun bayyana cewa girgizar ƙasar ta afku ne a wajen birnin Semnan, wanda ke gabashin Tehran, babban birnin Iran da nisan kusan kilomita 210.
An gano cewa girgizar ƙasar ta kai zurfin mita 35 a cikin ƙasa, wanda masana ke ganin hakan yana nuni da cewa ƙanƙanuwa ce.
Sai dai kuma masana sun kara da cewa irin waɗannan girgizar ƙasa da ba su da zurfi a cikin ƙasa, su kan fi haifar da tasiri sosai a saman ƙasa, rahoton GB News.
Iran na ci gaba da musayar wuta da Isra'ila
Wannan lamari ya zo ne a cikin lokaci mai cike da tashin hankali, yayin da Iran da Isra’ila ke ci gaba da musayar wuta da makamai masu linzami.
Rikicin ya fara ne daga farmakin gaggawa da Isra’ila ta kai Tehran a ranar Jumma’a da ta gabata, wanda ya haddasa mutuwa da raunata mutane da dama tare da lalata gine-gine da wuraren soji.

Asali: Getty Images
Hukumomin kasar Iran sun fara bincike
Sai dai wannan girgizar ƙasa da ta afku bayan an sauko sallar Juma'a ta ƙara jefa Iraniyawa cikin fargaba, musamman mazauna yankin Semnan da kewaye.
Har zuwa yanzu babu rahoton mutuwa ko babbar asara da girgizar ƙasar ta haddasa, sai dai hukumomi sun fara gudanar da bincike don tantance girman barna da kuma tabbatar da lafiyar jama'a.
Isra'ila ta kai hari wani asibiti a Tehran
A wani labarin, kun ji cewa ƙasar Iran ta sanar da cewa Isra'ila ta sake kai hari kan wani asibiti a Tehran, na uku tun faran ɓarkewar rikici a tsakaninsu.
Ta bayyana cewa harin da aka kai bai tsaya iya asibiti kawai ba, har da muhimman kayan aiki da ke taimaka wa marasa lafiya da jama’ar gari gaba ɗaya.
A cewar hukumomin Iran, asibitocin da aka kai wa hari a baya sun hada da asibitin da ke kusa da kan iyakar Yamma da Iraq da asibitin lardin Khuzestan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng