Masu Suyan Kosai Sun Samu Garabasa, Yobe Ta Ware Miliyoyi ga Masu Sana'o'i
- Gwamnatin Yobe ta amince da kashe Naira miliyan 460.83 domin tallafa wa mata masu ƙananan sana'o'i
- Majiyoyi sun bayyana cewa an yi hakan ne musamman masu soya ƙosai, da kayayyakin aikin sana'a
- Za a raba buhunan wake 1,780 tare da man girki, murhunan da ba sa hayaki, tukwane da kayan girki ga waɗanda za su amfana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Damaturu, Yobe - Gwamnatin Yobe ta amince da kashe Naira miliyan 460.83 domin tallafa wa mata masu ƙananan sana'o'i.
A cikin wadanda aka taimaka wa har da masu soya ƙosai, a faɗin jihar baki daya domin inganta tattalin arziki.

Source: Twitter
An amince da wannan ne a taron Majalisar Zartarwar Jihar da Gwamna Mai Mala Buni ya jagoranta a gidan gwamnati da ke Damaturu, cewar Punch.
Musabbabin taimakawa masu ƙananan sana'o'i
Kwamishinan Harkokin Cikin Gida, Yaɗa Labarai da Al'adu, Abdullahi Bego, ya ce shirin zai taimaka wa mata masu ƙananan sana'o'i ta hanyar samar musu da muhimman kayan aiki.
Ya ce majalisar ta amince da kashe Naira miliyan 460,828,450 domin sayen wake da za a raba wa mata masu ƙananan sana'o'i a matsayin tallafin ƙarfafa sana'arsu.
Bego ya bayyana cewa za a raba waken tare da man girki, murhunan da ba sa hayaki, tukwane da sauran kayan girki da ma'aikatar ƙirƙirar arziki ta riga ta tanada.
Ya ƙara da cewa jimillar buhunan wake 1,780 masu nauyin kilo 50 za a raba wa waɗanda aka zaɓa domin cin gajiyar shirin.
A cewarsa, wannan tallafi wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin Buni na inganta rayuwar mata tare da ƙarfafa ƙananan sana'o'i a faɗin jihar.
Bego ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da kashe Naira miliyan 364.48 domin sayen injinan niƙa na Yamaha GX 390 guda 1,000 domin rabawa jama'a.

Kara karanta wannan
"Shin Rasha ta kashe sanatan Amurka"; An fara nuna yatsa kan mutuwar aminin Trump
Ya ce an amince da wannan shiri ne ta hannun Ma'aikatar Ƙirƙirar Arziki, Ƙarfafa Tattalin Arziki da Samar da Ayyukan Yi domin tallafa wa al'ummar jihar.
Haka kuma, ya ce Majalisar Zartarwar ta amince da ayyuka da hidimomi da darajarsu ta kai Naira biliyan 73.32 a muhimman sassan tattalin arzikin jihar.
Ayyukan sun haɗa da kashe Naira biliyan 28.53 wajen sayen kayan aikin noma, Naira biliyan 23.97 domin manyan tituna biyu, da kuɗaɗen gidaje, kasuwanni da sauran ayyukan more rayuwa.
Yadda minista ya taya mahaifiyarsa tuyan kosai
An ji cewa Fadar Shugaban Kasa ta kare kananan sana'o'i, tana cewa akwai mutunci a cikinsu bayan kalaman Sanata Oluremi Tinubu.
Mai ba shugaban kasa shawara, Sunday Dare, ya ce an fahimci kalaman Uwargidan Shugaban Kasa ba daidai ba.
Fadar Shugaban Kasa ta ce sana'o'in akara, masara da kuli-kuli na samar wa miliyoyin 'yan Najeriya abin dogaro da kuma tallafa wa tattalin arziki.
Asali: Legit.ng
