Fashin bankin da ya girgiza Garin Abuja a karshen makon nan

Fashin bankin da ya girgiza Garin Abuja a karshen makon nan

A Ranar Asabar dinnan, 29 ga Watan Disamban 2019, wasu Miyagun mutane su ka nemi su yi fashi a wani bankin First Bank da ke Garin Abuja.

Wadannan ‘Yan fashi sun nemi su yi sata a banki ne da tsakar safe yayin da ido-ke-ganin-ido kuma a Ranar da kaf bankuna ke hutu da fitowa aiki.

A karshe jami’an tsaron da ke dankare a wannan yanki na Mpape inda ake da Barikin Sojojin kasa sun yi ram da wadannan Barayi masu karfin hali.

A kusa da Unguwar Mpape akwai Bankuna kusan shida. First Bank din shi ne na hudu a jerin bankunan kamar yadda rahoton Daily Trust ya bayyana.

Da safiyar Allah aka ji harbin bindiga bayan zuwan wadannan ‘Yan fashi bankin. Da zuwansu ne su ka budawa Jami’an ‘Yan sandan da ke aiki wuta.

Wadannan ‘Yan sanda ne su ka sanar da jami’ai abin da ke faruwa. A wata majiyar kuma, har ‘Yan fashin sun daure wani daga cikin Jami'an.

KU KARANTA: Ba na damuwa da sunan da 'Yan Najeriya za su kira ni - Buhari

“Barayin sun harbi ‘Dan Sanda kafin su shiga bankin. Jami’in ya budawa ‘Yan fashin wuta. An yi wasu mintuna ana wannan ba-ta-kashi.” Inji Wani.

Bayan mintuna kusan 40 da jin harbin ‘Yan fashin sai Dakarun ‘Yan Sanda da Sojoji su ka iso wurin, nan aka rutsa da Miyagun har kusan sa’a biyu.

Kafin nan an ga motoci cike da jami’an tsaron Sojoji a hanyar zuwa wurin. Daga nan mutanen Gari su ka tattara su ka nufi bankin domin ganewa idanunsu.

A lokacin da ‘Yan Sandan su ka dura, an kashe wani daga cikin ‘Yan fashin, sannan an kama uku. Wani mutum ya fito daga rufin ginin ya sallama kansa.

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, wani ya shaidawa ‘Yan jarida cewa akwai hannun Ma’aikatan bankin a fashin, amma ba a saci ko sisi ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel