Sulhu tsakanin Iran da Amurka: Ayatollah Khamenei Ya Kafawa Trump Sharuda

Sulhu tsakanin Iran da Amurka: Ayatollah Khamenei Ya Kafawa Trump Sharuda

  • Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce rikicin Iran da Amurka ya samo asali ne daga banbancin muradun siyasa da manufofi
  • Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana wasu sharuda da ya ce dole sai kasar Amurka ta cika su kafin ta iya samun dangantaka mai kyau da Iran
  • Khamenei ya fito da tarihin mamayar ofishin jakadancin Amurka a shekarar 1979 da ya ce ta zama rana ta tarihi ga Iran tare da tasiri tsakanin kasashen biyu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran – Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya bayyana cewa rikicin dake tsakanin Iran da Amurka ba rikici bane na dan lokaci ko siyasa ta wucin gadi.

Ya fitar da wasu sharuda da ya ce idan Amurka ta cika su za a daina zaman doya da manja tsakanin Tehran da Washington.

Kara karanta wannan

Burna Boy: Yadda fitaccen mawakin Najeriya ya gano Musulunci ne gaskiya

Ali Khamenei, Donald Trump
Jagoran Iran, Khamenei da shugaban Amurka, Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ayatollah Khamenei ya bayyana hakan ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin bayan ganawa da daliban jami’a a Tehran.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya gana da dalibai ne a taron tunawa da ranar 4, Nuwamban 1979, ranar da daliban Iran suka mamaye ofishin jakadancin Amurka.

Sharudan sulhu da Iran ta kafawa Amurka

Khamenei ya ce kalaman da wasu jami’an Amurka ke yi na son yin haɗin gwiwa da Iran ba su da ma’ana muddin suna ci gaba da goyon bayan mummunan tsarin Yahudawa.

A cewarsa:

“Ba za a iya yin haɗin kai da Iran ba yayin da suke tallafa wa wannan tsarin da duniya ke tir da shi.
"Idan har za su daina goyon bayan Isra’ila, su rufe sansanonin sojoji daga yankin, kuma su daina tsoma baki a kasashenmu, to za a iya sake nazari kan batun dangantaka.”

Sai dai rahoton Tehran Times ya ce jagoran ya ce hakan ba wani abu bane da ake iya tsammani a yanzu ko nan gaba kaɗan.

Kara karanta wannan

Najeriya da Amurka: Abdulsalami Abubakar ya fadi me ya ke ganin shi ne mafita

Tarihin mamayar ofishin jakadancin Amurka

Jagoran ya yi bayani kan mamayar ofishin jakadancin Amurka a ranar 4, Nuwamba, 1979, inda ya ce wannan rana ce da ta zamo abin alfahari ga al’ummar Iran.

Jagoran Iran, Khamenei
Ali Khamenei da wasu jagororin Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya ce matakin daliban a lokacin ya samo asali ne daga fushin jama’a bayan gwamnatin Amurka ta karɓi tsohon Sarkin Iran, Mohammad Reza Pahlavi da aka kifar da mulkinsa a juyin juya halin kasar.

Khamenei ya ce:

“Daliban sun mamaye ofishin ne na tsawon kwanaki biyu zuwa uku domin nuna fushin jama’a,
"Amma daga baya sun gano takardu da suka tabbatar cewa ofishin yana cike da shirin kifar da sabuwar gwamnati.”

'Yan Shi'a sun soki kalaman Trump

A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar 'yan Shi'a ta Najeriya, IMN ta yi Allah wadai da kalaman Donald Trump kan Najeriya.

Shugabansu na Najeriya, Ibrahim Zakzaky ya ce ikirarin da Trump ya yi na cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Kiristoci: Peter Obi ya fadi matsayarsa kan yunkurin Amurka na kawo farmaki Najeriya

Kungiyar IMN ta bukaci 'yan Najeriya su yi watsi da kalaman Trump da za su iya jawo rabuwar kawuna a cikin kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng