Yakin Iran: Trump Ya Ragargaji Fafaroma Leo a Sabon Sakon da Ya Fitar

Yakin Iran: Trump Ya Ragargaji Fafaroma Leo a Sabon Sakon da Ya Fitar

  • Shugaba Donald Trump na cigaba da caccakar Fafaroma Leo XIV kan gargadin da ya masa game da yake-yake da kai hare-hare kasashe
  • A wannan karon, Donald Trump ya fitar da wani sako game da Iran, inda ya bukaci a sanar da Fafaroman idan har bai san abin da ya faru ba
  • A yanzu haka dai Fafaroma Leo ya taho nahiyar Afrika domin ya ziyarci wasu kasashe hudu kafin ya koma, inda ya fara da kasar Algeria

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake sukar Fafaroma Pope Leo XIV kan kiransa na kawo ƙarshen rikice-rikicen duniya, inda ya zarge shi da yin watsi da yadda Iran ta murƙushe masu zanga-zanga a farkon wannan shekara.

Trump ya yi magana ne bayan Fafaroma Leo ya mayar masa da martani yana cewa ba ya jin tsoron kowane mutum wajen fadin gaskiya.

Kara karanta wannan

Fafaroma Leo ya shiga masallacin Algeria bayan musayar yawu da Donald Trump

Shugaba Donald Trump da Fafaroma Leo XIV
Shugaba Donald Trump a hagu, Fafaroma Leo a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Yahoo News ya nuna cewa a wannan karon Donald Trump ya caccaki Fafaroma ne kan zanga-zangar da aka yi a Iran a karshen 2025.

Trump ya caccaki Fafaroma kan Iran

A wata sabuwar dambarwa, Donald Trump ya sake kakkausar suka ga Fafaroma Leo, inda ya bukaci a isar masa da sakon da ya fitar.

A sakon da ya fitar, rahoton Politico ya nuna cewa Trump ya ce:

“Wani ya gaya wa Fafaroma Leo cewa Iran ta kashe aƙalla mutane 42,000 marasa laifi kuma marasa makami a cikin wata biyu da suka gabata, kuma ba zai yiwu a amince Iran ta mallaki makamin nukiliya ba.”

Amurka da Isra’ila sun fara yaƙi da Iran a ƙarshen watan Fabrairun 2026, da nufin dakile shirin nukiliyar Tehran da kuma ikon ta na ƙera makaman nukiliya amma a halin yanzu an tsagaita wuta na makonni biyu.

Batun zanga-zanga a Iran

An yi zanga-zanga a Iran ne a ƙarshen watan Disamban 2026 sakamakon matsalar tattalin arziki, amma daga baya ta rikide zuwa bore mai faɗi kan tsarin mulkin Jamhuriyar Musulunci.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: Gwamnatin Amurka ta sake hurawa Fafaroma Leo wuta kan Trump

Shugaba Donald Trump ya yi zargin cewa jami’an tsaron kasar sun mayar da martani cikin nuna ƙarfi tare da murƙushe masu zanga-zangar.

Masu zanga-zangar Iran
Wasu masu zanga-zangar goyon bayan gwamnatin Iran a Tehran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Laifin Fafaroma wajen Trump

Fafaroma Leo, yayin wata addu’ar zaman lafiya a St. Peter’s Basilica da ke Roma, ya yi kira da a kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe, inda ya fi mai da hankali kan rikicin da ya shafi Iran.

Fafaroman, wanda shi ne na farko daga Amurka, ya soki barazanar Trump kan Iran, yana mai kiran lamarin da “abin da ba za a yarda da shi ba kwata-kwata,” abin da ya harzuka Trump.

Mataimakin Trump ya soki Fafaroma

A wani labarin, kun ji cewa Mataimakin shugaban kasar Amurka, JD Vance ya yi wa Fafaroma Leo martani kan sukar Donald Trump.

JD Vance ya bukaci Fafaroma Leo ya mayar da hankali kan lamuran addini maimakon sukar Trump da neman kawar da hankalin shi kan lamuran mulki.

Baya ga haka, JD Vance ya kare shugaba Trump kan shigar Yesu Almasihu da ya yi yana nuna kamar zai warkar da wani maras lafiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng