Fafaroma Leo Ya Shiga Masallaci bayan Musayar Yawu da Donald Trump
- Rahotanni sun nuna cewa Fafaroma Leo XIV ya kai ziyara wani katafaren masallacin Juma'a a kasar Algeria, inda ya yi kira kan zaman lafiya
- Ya kai ziyara masallacin yayin da ya taho nahiyar Afrika a ranar Litinin, 13 ga watan Afrilun 2026 domin ganawa da wakilan addini a wasu kasashe
- Tsohon shugaban kasar Algeria, Abdelaziz Bouteflika ne ya gina masallacin da a yanzu haka yake iya daukar mutane akalla 120,000
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Algeria - Fafaroma Leo XIV ya fara ziyararsa a Afirka zuwa babban masallacin Algeria, inda ya jaddada muhimmancin zaman lafiya a duniya.
Shugaban masallacin, Mohamed Mamoun al Qasim na cikin wadanda suka tarbi Fafaroman, wanda ya yi masa maraba cikin girmamawa.

Source: Getty Images
Bayanin Fafaroma Leo XIV a Algeria
Rahoton Vatican News ya nuna cewa Fafaroman ya nuna godiya bisa yadda aka tarbe shi yayin fara ziyarar a wajen ibada mai matukar muhimmanci.
Ya kuma tuna dangantakarsa da kasar ta hanyar Augustine na Hippo, yana bayyana Algeria a matsayin kasa mai alaka da addini.
Fafaroman ya jaddada muhimmancin tsayuwa kan gaskiya, daraja kowane dan Adam, tare da bayyana cewa samar da zaman lafiya aiki ne da ya shafi kowa.
Yabon Fafaroma ga masallacin
Fafaroman ya kuma nuna muhimmancin bangaren yada ilimi da masallacin ke da shi, yana mai cewa bunkasa ilimin dan Adam na taimakawa wajen fahimtar rayuwa da sanin darajar dan Adam.
A karshe, ya yi addu’a ga mutanen Algeria da dukkan kasashe, yana fatan zaman lafiya, adalci, sulhu da yafiya su bunkasa a tsakanin al’umma.
Rahoton the Guardian ya nuna cewa a yayin ziyarar, Fafaroman ya samu rakiyar George Jacob Koovakad da babban Faston Algeria, Jean-Paul Vesco.
Abubuwan da suka yi sun hada da zagaye masallacin, daukar hoto da kuma sanya hannu a wani littafi, inda ya rubuta:
“Allah Madaukaki Ya kiyaye mutanen Algeria da dukkan bil’adama, cikin zaman lafiya da ‘yanci.”

Source: Getty Images
Tarihin masallacin da Fafaroma ya ziyarta
An gina babban masallacin ne bisa umarnin tsohon shugaban Algeria, Abdelaziz Bouteflika, a matsayin wani bangare na hangen nesansa.
Wasu rahotanni sun nuna cewa masallacin ne na uku mafi girma a duniya, kuma yana iya daukar masu ibada har mutum 120,000.
Hasumiyar babban masallacin tana da tsayin mita 267, wanda ya sa ita ce mafi tsayi a duniya a yau, kuma tana dauke da ado kala-kala.
Baya ga matsayin sa na wurin ibada, masallacin yana dauke da abubuwan al’adu da na ilimi kamar dakin karatu, cibiyar bincike, gidajen tarihi, ofisoshi, lambuna, gidajen cin abinci da filayen ajiye motoci da sauransu.
Amurka ta gargadi Fafaroma Leo
A wani labarin, mun kawo muku cewa Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ya gargadi Fafaroma Leo kan sukar Donald Trump.
Hakan na zuwa ne bayan musayar yawu da aka yi bayan Fafaroma ya caccaki Donald Trump kan yakin da ya kaddamar a kasar Iran.
JD Vance ya kare shigar Yesu Almasihu da Trump ya yi a ranar Litinin, inda ya nuna kan shi yana kai dauki ga maras lafiya a wani hoto.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

