Yadda ake Shirin Hana Trump Sayarwa Isra'ila Makamai a Majalisar Amurka
- Ana cigaba da samun masu fada a ji a Amurka na nuna adawa game da alakar kasar da Isra'ila kan sayar wa Tel Avi makamai da sauransu
- Rahotanni sun nuna cewa Sanata Bernie Sanders ya yi alƙawarin tilasta dakatar da sayar da makaman Amurka ga Isra’ila a majalsar kasar
- Bernie Sanders ya kasance na gaba-gaba wajen caccakar yake-yake da Donald Trump ke yi da kuma hare-haren Isra'ila a Gaza da Lebanon
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - An fara kokarin tilasta Amurka ta daina alakar sayar da makamai da gwamnatin Isra'ila da Benjamin Netanyahu ke jagoranta.
Hakan na zuwa ne bayan hare-hare da Benjamin Netanyahu ke kai wa yankunan kasar Lebanon da Gaza, inda dubban mutane suka mutu.

Source: Facebook
Legit Hausa ta gano cewa Sanata Bernie Sanders ne ya sha alwashin tabbatar da yanke alakar saye da sayarwa kan makami tsakanin kasashen a wani sako da ya wallafa a X.
Batun hana Amurka alaka da Isra'ila
Sanatan Amurka Bernie Sanders ya ce zai tilasta wa Majalisar Dattawa ta kada ƙuri’a domin hana wata babbar yarjejeniyar sayar da makamai ga Isra’ila.
Ya yi magana ne yana ƙara tsananta sukar da yake yi kan goyon bayan da Amurka ke bai wa gwamnatin Benjamin Netanyahu, wadda ya zarga da aikata kisan kare dangi a Gaza.
“A wannan makon, zan tilasta a kada ƙuri’a kan wata doka da za ta hana sayar da bama-bamai da kayan fada na kusan Dala miliyan 500 ga rundunar sojin Isra’ila,”
In ji Sanata Sanders
Rahoton Anadolu Agency ya nuna cewa ya ƙara da cewa:
“Gwamnatin Netanyahu da ta aikata kisan kare dangi a Gaza, ba ta buƙatar ƙarin tallafin soji daga harajin ‘yan Amurka.”

Source: Getty Images
Rahotanni sun nuna cewa Sanata Sanders ba ya cikin babbar jam’iyya a Amurka amma yana aiki tare da ‘yan Democrat, wanda ake hasashe da su zai hada kai a majalisa.
Sukar Sanders ga Isra'ila a baya
Wannan mataki na zuwa ne bayan irin ƙoƙarin da Sanders ya saba yi na kalubalantar sayar da makaman Amurka ga Isra’ila ta hanyar amfani da dokar da ke ba Majalisar Dattawa damar yin ƙuri’a kan irin waɗannan yarjejeniyoyi.
A watan Janairun 2026, Sanders ya gabatar da irin wannan ƙuduri domin hana sayar da bama-bamai na kusan Dala miliyan 660 ga Isra’ila.
Wasu ‘yan majalisar Amurka ma suna matsa lamba cewa Amurka ta dakatar da bai wa Isra’ila makamai tare da kawo ƙarshen duk wata rawar da take takawa a Tel Aviv.
Uganda za ta taimaki Isra'ila
A wani labarin, kun ji cewa babban hafsun sojan kasar Uganda ya bayyana aniyar kasarsa ta taimakwa gwamnatin Benjamin Netanyahu da dakaru.
Shugaban sojojin ya sanar da cewa za su yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin sun taimakawa kasar Isra'ila da dakaru sun kare kansu.
Ya bayyana cewa za su iya ba Isra'ila sojoji 100,000 su kare su daga barazanar Iran tare da tura karin dakaru 500,000 su kwace Tehran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

