Duk da Kisan Palasdinawa, Amurka Na Shirin Kawo Cikas kan Tsagaita Wuta a Gaza
- Ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an tsagaita wuta kan yaƙin da Isra'ils take yi da ƙungiyar Hamas a zirin Gaza
- Kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya ya shirya kaɗa ƙuri'a kan ƙudirin da ke neman ganin an dakatar da yaƙi a Gaza
- Sai dai, akwai yiwuwar Amurka wacce ƙawar Isra'ila ce za ta iya hana ƙudirin wucewa ta hanyar hawa kujerar na ƙi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Amurka - Kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya zai kaɗa ƙuri'a a ranar Laraba kan ƙudirin da ke kira da a tsagaita wuta a zirin Gaza.
Ƙudirin ya kuma buƙaci a bayar da cikakkiyar damar kai kayan agajin jinƙai a zirin Gaza.

Asali: Getty Images
Jaridar The Times of Israel ta rahoto cewa ana sa ran ƙudirin ba zai yi nasara ba sakamakon yiwuwar turjiya daga Amurka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a kaɗa ƙuri'ar neman tsagaita wuta a Gaza
Wannan zai kasance ƙuri'ar farko da kwamitin mai mambobi 15 zai kaɗa tun watan Nuwamba, lokacin da Amurka babbar abokiyar Isra’ila, ta hana wani ƙudiri da ke kiran da a dakatar da faɗa.
Sabon ƙudirin na buƙatar dakatar da yaƙi kai tsaye, ba tare da wani sharaɗi ba, tare da ɗorewar zaman lafiya a Gaza wanda dukkan ɓangarori za su mutunta.
Haka kuma ƙudirin na kira da a sako dukkan fursunoni da aka kama, cikin girmamawa da gaggawa, ba tare da wani sharaɗi ba, waɗanda Hamas da sauran ƙungiyoyi ke riƙe da su.
Ƙudirin ya bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin mara daɗi kuma mai muni, sannan yana buƙatar a daina kawo cikas wajen shigar da kayan agajin jinƙai zuwa Gaza.
Za a ƙada ƙuri’a kan ƙudirin ne da ƙarfe 4:00 na yamma agogon yankin New York a ranar Laraba (8:00 na dare agogon GMT).
Amurka na iya kawowa Gaza cikas
Sai dai, wasu jakadu sun bayyana cewa suna sa ran Amurka za ta yi amfani da ikon da take da shi na hawa kujerar na ƙi, don hana wucewar ƙudirin.
Sun ƙara da cewa wakilan ƙasashe 10 da aka zaɓa a matsayin mambobi na wucin gadi a kwamitin sun yi ƙoƙarin tattaunawa da Amurka don cimma matsaya, amma hakan bai yi nasara ba.
An taso Isra'ila a gaba kan yaƙi a Gaza
Isra’ila na fuskantar ƙarin matsin lamba daga ƙasashen duniya waɗanda suka nemi kawo ƙarshen yaƙin da take yi a Gaza, wanda ya samo asali ne daga harin da Hamas ta kai cikin Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Asali: Getty Images
Matsin lambar na ƙaruwa ne saboda matsalar rabon kayan agaji a Gaza, wanda Isra’ila ta hana fiye da watanni biyu, kafin ta amince da wasu motoci kaɗan na majalisar ɗinkin duniya su shiga a tsakiyar watan Mayu.
Sai dai, majalisar ɗinkin duniya ta ce hakan bai wadatar ba domin buƙatar al’ummar Gaza ta wuce nan.
Birtaniya ta raba hanya da Isra'ila
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin ƙasar Birtaniya ta ɗauki mataki kan Isra'ila saboda yaƙin da take yi a Gaza.
Gwamnatin ta dakatar da tattaunawar cinikayya da Isra'ila saboda yadda take gudanar da yaƙinta a Gaza.
Wannnan matakin na zuwa ne bayan sojojin Isra'ila sun yi wa dubunnan Palasɗinawa kisan gilla.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng