"Ba Mu Ciki": Amurka Ta Bayyana Matsayarta Kan Rikicin Iran da Isra'ila, Ta Yabawa Sojoji

"Ba Mu Ciki": Amurka Ta Bayyana Matsayarta Kan Rikicin Iran da Isra'ila, Ta Yabawa Sojoji

  • Yayin da ake ci gaba da rikici tsakanin Iran da Isra'ila, gwamnatin Amurka ta bayyana matsayarta kan lamarin
  • Shugaban Amurka, Joe Biden ya tabbatar da cewa kasarsa ba za ta shiga fadan kasashen guda biyu ba a halin yanzu
  • Wannan na zuwa ne bayan Iran ta kai harin ramuwar gayya kan Isra'ila a jiya Asabar 13 ga watan Afrilu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Amurka - Shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya bayyana matsayarsa kan rikicin Iran da Isra'ila.

Biden ya tabbatarwa Fira Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu cewa ba zai shiga fadar Iran da kasar ba, cewar CNN.

Amurka ta fayyace matsayarta kan rikicin Iran da Isra'ila
Amurka ta ce sojojinta ba za su shiga fadan Iran da Isra'ila ba. Hoto: Joe Biden.
Asali: Twitter

Wane bangare Amurka ke goyon baya?

Kara karanta wannan

"Abin takaici ne", Shehu Sani ya magantu game da harin da Iran ta kai kan Isra'ila

Shugaban na Amurka ya ce yadda Isra'ila ta yi nasarar kakkabe jirage marasa matuka ya nuna karfin sojoji da suke da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya tabbatar da cewa Amurka ba za ta shiga fadan Iran da Isra'ila ba bayan kai harin ramuwar gayya a jiya Asabar 13 ga watan Afrilu.

Jami'an tsaron Isra'ila sun tabbatar da kakkabo jiragen da makamai masu linzami tare da taimakon kasar Amurka, cewar rahoton New York Post.

Aƙalla jirage marasa matuka 300 ne Isra'ila ta tarwatsa tare da sojojin Amurka da kuma Burtaniya wanda Iran ta harba su.

Musabbabin harin Iran kan Isra'ila

Wannan na zuwa ne bayan Iran ta kai harin ramuwar gayya kan Isra'ila game da harin da kai mata a baya.

A kwanakin baya Isra'ila ta kai mummunan hari kan ofishin jakadancin Iran da ke kasar Syria.

Kara karanta wannan

An shiga jimami yayin da fitaccen dan jarida a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Harin ya yi sanadin mutuwar manyan jami'an gwamnatin kasar Iran da ke Syria inda ta sha alwashin daukar mataki.

Iran ta dauki matakin harba jiragen yaki marasa matuka duk da kokarin kawo sulhu da Majalisar Dinkin Duniya ta yi domin dakile rikicin.

Sani ya magantu kan Iran da Isra'ila

A baya, mun ruwaito muku cewa Sanata Shehu Sani ya yi martani kan harin Iran a kasar Isra'ila a jiya Asabar 13 ga watan Afrilu.

Shehu Sani ya ce abin da ya faru ya nuna gazawar shugabannin duniya inda ya koka kan yadda yaƙi ke neman tarwatsa Gabas ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel