Bayan Zuwan Tawagar Tinubu Nijar, ECOWAS Tana Ganawa kan Matsayar Kasashe 3

Bayan Zuwan Tawagar Tinubu Nijar, ECOWAS Tana Ganawa kan Matsayar Kasashe 3

  • Kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar sun fice daga ECOWAS, hakan ya sa kungiyar ke taro a Ghana don tattauna illolin hakan
  • Taron zai gudana na tsawon kwanaki biyu, inda za a duba tasirin ficewar kasashen da kuma matakan da za a dauka a gaba
  • ECOWAS ta ce za ta kafa tsarin tattaunawa da kasashen ukun domin gano yadda za a ci gaba da hulɗa da su duk da matakin nasu
  • Kasashen AES sun kakabawa kaya daga ECOWAS harajin kashi 0.5, duk da kokarin ECOWAS na ci gaba da hadin gwiwa da su

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Accra, Ghana - Kasashen da ke kungiyar ECOWAS za su gana a Ghana a yau Talata domin tattauna ficewar ƙasar Nijar, Mali da Burkina Faso daga kungiyar.

Taron zai gudana na tsawon kwana biyu, daga ranar Talata zuwa Laraba 23 ga watan Afrilun 2025 domin nazarin matakan da za a dauka.

Za a gana bayan kasashen Nijar sun fice a ECOWAS
Kungiyar ECOWAS za ta gana Ghana kan matsayar Nijar, Mali da Burkina Faso. Hoto: @ecowas_cedeao.
Asali: Getty Images

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar yau Talata, ta ce za a tattauna hanyoyin ficewar kasashen uku da yadda hakan zai shafi ayyukanta, cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nijar, Mali sun ƙaƙaba haraji kan kasashen ECOWAS

A makonni uku da suka wuce, kasashen AES sun kakabawa kaya daga ECOWAS harajin shigo da kaya kashi 0.5 bisa dari.

Harajin na shafi duka kaya daga ECOWAS da ke shigowa kasashen uku sai dai kayan agajin jin kai ne kadai aka keɓe.

Wannan matakin ya saba da kokarin ECOWAS na tabbatar da 'yancin zirga-zirgar kaya duk da ficewar kasashen uku daga kungiyar.

Sai dai sabuwar yarjejeniyar AES na nufin tara kudin shiga domin tallafa wa ayyukan hadin gwiwar kasashen ukun.

Za a tattauna bayan Nijar, Mali da Burkina Faso sun fice daga ECOWAS
Kungiyar ECOWAS za ta wata ganawa domin neman mafita da Nijar, Mali da Burkina Faso suka fice daga cikinta. Hoto: @ecowas_cedeao.
Asali: Twitter

Musabbabin ganawar da ECOWAS ke yi a Ghana

Rahotanni sun ruwaito cewa kasashen uku da ke mulkin soja sun bayyana ficewarsu daga kungiyar tun farkon wannan shekara.

A lokacin, ECOWAS ta fitar da ka’idojin alakarta da kasashen uku da kuma matakan wucin gadi da za a aiwatar.

Kungiyar ta ci gaba da amincewa da ciniki da zirga-zirgar mutane ba tare da biza ba tsakanin kasashen da suka fice da sauran mambobi.

ECOWAS ta kara da cewa za ta kafa wata cibiya don saukaka tattaunawa da kowane daga cikin kasashen ukun da suka fice.

Sai dai yanzu, kasashen mambobi za su tattauna da kasashen ukun a Accra kan makomar dangantaka tsakaninsu.

Sanarwar ta ce:

“Za a gudanar da taron ne don nazarin ficewar Burkina Faso, Mali da Nijar daga kungiyar ECOWAS.
“Abubuwan da za a tattauna sun hada da matakan ficewar da kuma yadda zai shafi cibiyoyin ECOWAS da ke cikin kasashen ukun.”

Haka kuma, za a tattauna sauran batutuwa da suka shafi muhimmancin yankin gaba daya, Punch ta ruwaito.

Tinubu ya tura tawaga zuwa Nijar

Kun ji cewa Gwamnatin Bola Tinubu ta tura ministan harkokin waje, Yusuf Maitama Tuggar, zuwa Jamhuriyar Nijar domin isar da sakon shugaban kasa.

An ce ziyarar na zuwa ne bayan rikicin juyin mulkin, Najeriya na kokarin farfado da dangantaka da hadin gwiwar tsaro da kasuwanci da makwabciyarta.

Tun da Janar Abdourahamane Tchiani ya kifar da Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023, alakar da ke tsakanin Najeriya da Nijar ta tabarbare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.