Masallacin Harami ya karbi masu Umarah na farko daga wajen kasar Saudiyya

Masallacin Harami ya karbi masu Umarah na farko daga wajen kasar Saudiyya

- Ma'aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta ce ta shirya tsaf don tabbatar da anyi aikin Umarah lafiya

- Ma'aikata 20,000 da masallata 60,000 ke samun shiga masallacin Harami a kullum a ci gaba da bin matakan kariya

- An dauki ma'aikata 4,000 don gudanar da aikin tsaftace masallatan da masu sa ido

Masallacin Harami a ranar Laraba ya karbi kashin farko na masu aikin Umarah daga wajen Saudiyya a mataki na uku na yunkurin dawo da ayyukan Umarah da ziyarar masallatan Harami.

A mataki na uku, masu aikin Umarah 20,000 da masallata 60,000 ake bari shiga masallacin a kowace rana a yunkurin kariya daga annobar Corona don tabbatar da lafiya.

Masallacin Harami ya karbi masu aikin Hajji na farko daga wajen Saudiyya
Masallacin Harami ya karbi masu aikin Hajji na farko daga wajen Saudiyya. Hoto: www.aljazeera.com / AP
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zaɓen Amurka: Magoya bayan Trump sunyi zanga-zanga a ofishin ƙidayar ƙuri'u ta Arizona

Ma'aikatar Hajji da Umarah ta kammala shirye shirye yayin da take karbar baki daga sassan duniya don daukar matakan kariya don kare yaduwar Corona.

Ta bayyana dukkan shirinta na bada kariya don tabbatar da masu aikin Umarah sunyi aikin cikin koshin lafiya da yanayi mai dadi a cewar rahoton da Daily Trust ta wallafa.

KU KARANTA: Wilbur: Hotunan karen da ya lashe zaɓen kujerar magajin gari a Amurka

A cewar shugaban masallatan haramin, Sheikh Abdulrahman Al- Sudais, an dauki ma'aikata 4,000 maza da mata da aka rabawa kayan aiki da kuma fiye da Injina 470 don tsaftace da kuma kashe kwayoyin cuta a Masallacin mai tsarki da kuma bibiyar aikin tsabtace masallatan.

A wani labarin, hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa na Jihar Kano ta sanar da cewa tana shirin daukan sabbin ma'aikata a kalla 700 don kara wa kan 2,500 da ta ke da su a jihar a halin yanzu.

Shugaban na KAROTA, Baffa Dan'agundi ne ya sanar da hakan yayin da ya ke zantawa da 'yan jarida a ranar Laraba a jihar Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164