Firaministan Pakistan ya yi kira ga tsaurara hukunci kan masu batanci ga Annabi

Firaministan Pakistan ya yi kira ga tsaurara hukunci kan masu batanci ga Annabi

- Firaministan Pakistan ya yi kira ga hadin kai tsakanin kasashen musulmai kan batanci ga Annabi S.A.W

- Ya bayyana cewa, ya kamata kasashen yammaci su sanya tsauraran hukunci kan masu batanci ga Annabi

- Ya kuma bukaci hakan kamar yadda kasashen yammaci ke hukunta masu karyata kisan kiyashi ga Yahudawa

Firayim Ministan Pakistan Imran Khan ya yi kira ga kasashen Yammacin duniya da su tsaurara hukunci kan laifin cin mutuncin Annabi, kamar yadda suke yi kan masu musanta kisan kiyashi kan Yahudawa.

A jawabin da ya yi wa ‘yan kasar ta gidan talabijin daga babban birnin Islamabad, a ranar Litinin, Khan ya ce zai jagoranci kamfen din kasashen da ke da rinjayen Musulmai don "shawo kan” kasashen Yammacin duniya kan batun yin batanci ga Annabi Muhammad.

"Ya kamata mu bayyana dalilin da ya sa hakan ke kona mana rai, kawai da sunan 'yancin fadar albarkacin baki suna cin mutuncin Annabi," in ji Khan.

KU KARANTA: Wani jigon jam'iyyar APC ya bukaci Buhari ya gaggauta tsige Dr Pantami

Firaministan Pakistan ya yi kira ga tsaurara hukunci kan masu batanci ga Annabi S.A.W
Firaministan Pakistan ya yi kira ga tsaurara hukunci kan masu batanci ga Annabi S.A.W Hoto: azvision.az
Asali: UGC

"Lokacin da kasashen Musulmi 50 za su hada kai su ce wannan, su ce idan wani abu makamancin haka ya faru a kowace kasa, to za mu kaddamar da kauracewar kasuwanci a kansu ba za mu sayi kayansu ba, hakan zai yi tasiri."

Yana magana ne bayan an kwashe kwanaki ana zanga zanga a fadin kasar ta Pakistan ga magoya bayan wata jam’iyyar masu kishin Islama da ke fushi da yadda Faransa ke karfafa ‘yancin wallafa zane-zanen batanci na Annabi Muhammad.

Duk da cewa a yanzu gwamnati ta haramta jam’iyyar (Tehreek-e-Labbaik Pakistan) amma Mista Khan ya bayyana karara cewa ya yi tir da tarzomar da ta barke akan tituna.

Tun a watan Nuwamba, TLP ta bukaci Pakistan da ta kori jakadan Faransa a kan kalaman da Macron ya yi inda ya kare hakkin bugawa don sake buga hotunan Annabi Muhammad, aikin da wasu Musulmai suka ce "sabo ne".

Batanci ga Annabi magana ce mai mahimmanci a kasar Pakistan, inda wasu nau'ikan laifin zasu iya kai ga hukuncin kisa.

Tun daga 1990, akalla mutane 78 aka kashe a cikin wasu tashe-tashen hankula da wasu hare-hare da suka shafi zargi na batanci, a cewar alkaluman Al Jazeera.

KU KARANTA: Lai Mohammed ya caccaki masu son a raba kasa, ya ce rikici na bullowa zasu tsere

A wani labarin, Shugaban Mabiya Shi’a na Kungiyar Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (IMN), Sheikh Ibraheem Zakzaky ya raba kayan abinci na miliyoyin Nairori ga mabukata albarkacin watan Azumin Ramadan, Aminiya ta ruwaito.

Dan sa Muhammad Ibraheem Zakzaky ne ya jagoranci shirin rabon kayan abincin da suka hada da buhunan Shinkafa da Sukari da Masara da Gero a madadin mahaifin nasa.

Awata takarda da ya sanya wa hannu, Muhammad Ibraheem Zakzaky ya ce mahaifin nasa ya bayar da umarnin rabon kayan Azumin ne ga mabukata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel