An Harbe Tsohon Firam Ministan Pakistan, Imran Khan, Bidiyo ya Nuna

An Harbe Tsohon Firam Ministan Pakistan, Imran Khan, Bidiyo ya Nuna

  • An yi yunkurin kashe tsohon Firai Ministan kasar Pakistan ranar Alhamis waje zanga-zanga
  • An garzaya da Imran Khan asibiti inda ake zargin harsashi ne ya samesa a kauri sakamakon harin
  • Shugaban kasar Pakistan ya yi Alla-wadai da wannan harin kisa da aka kaiwa Imran Khan

Lahore - Wani dan bindiga dadi ya budewa tsohon Firai Ministan kasar Pakistan, Imran Khan, wuta yayinda yake jagorantar zanga-zanga a gabashin kasar, Wazirabad ranar Alhamis.

Babban hadiminsa, Raoof Hasan, ya bayyanawa AFP cewa an yi yunkurin kashesa ne amma ba'a samu nasara ba.

Imran Khan ya samu rauni harsashi a kafa.

Imran Khan
An Harbe Tsohon Firam Ministan Pakistan, Imran Khan, Bidiyo ya Nuna Hoto: Imran Khan
Asali: AFP

Wani dan jam'iyyar PTI ya bayyana cewa akalla mutum hudu suka jikkata a harin, rahoton BBC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An garzaya da Imran Khan asibiti a Lahore, Kakakin jam'iyyar ya bayyana game da rauni da ya samu a kauri.

Kara karanta wannan

Atiku Fa Aikinsa Sayar Da Ruwan Gora, Za Muyi Masa Ritaya Ya Koma Dubai: Kashim Shettima

Wani jigon jam'iyyar kuma Ministan lafiya, Yasmeen Rashid, yace Khan na cikin koshin lafiya.

An damke wanda ya kai harin

Jami'an yan sanda sun saki bidiyon damke mutumin da yayi harbin inda suka ce ya yi kokarin kashe tsohon Firai Ministan ne.

Yayinda aka tambayi mutumin shin me yasa yayi harbin, yace:

"Yana batar da mutane. Ina son in kasheshi. Na yi kokarin kashe shi."

Firai Ministan kasa, Shehbaz Sharif, ya yi Alla-wadai da wannan hari kuma yayi umurnin gudana da binciken gaggawa.

Hakazalika Shugaban kasa Arfi Alvi a sakn jajensa yace wannan yunkurin kasheshi akayi.

Yace:

"Ina Alla-wadai da harbin Shugaban PTI, Imran Khan, da kakkausan murya. Na umurci ministan harkokin cikin gida ya bani rahoton gaggawa kan lamarin."
"Ina addu'a samun lafiyar shugaban PTI da sauran wadanda suka jikkata."

Hukumomin Saudiyya sun haramta wa mazan kasar auren matan Pakistan

A wani labarin daban, An haramta wa mazan Saudi auren daga auren matan Pakistan, Bangladesh, Chadi da Burma.

Kara karanta wannan

Addu'a Muke Bukata Daga Amurka Ba Wai Su Tsorata Mu Ba, Ministan Buhari

Life in Saudi ta ruwaito cewa, an sanar da hakan ne don hana mazan Saudi karfin guiwar auren mata daga kasashen ketare.

'Yan kasar Saudi dake son auren matan kasashen ketare, da farko dai za su nemi takardar shaidar amincewa daga sananniyar hukumomin gwamna, tare da shigar da bukatar auren a inda ya dace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel