IMF Ta Damu Kan Yadda Tinubu Ya Dawo da Tallafin Mai a Boye, Ta Jero Matsaloli

IMF Ta Damu Kan Yadda Tinubu Ya Dawo da Tallafin Mai a Boye, Ta Jero Matsaloli

  • Yayin da 'yan Najeriya ke kokawa kan cire tallafin mai, hukumar IMF ta nuna damuwa kan halin da ake ciki
  • Hukumar ta ce yadda Bola Tinubu ya dawo da tallafin mai a sirrance babu abin da zai tsinanawa kasar sai asara kawai
  • Ta bayyana cewa kasar za ta yi asarar fiye da rabin kudin shiga da ta ke tsammanin samu bayan dawo da tallafin a boye

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hukumar ba da lamuni da duniya (IMF) ta nuna damuwa kan yadda Bola Tinubu ya dawo da tallafin mai a boye.

Hukumar ta ce dawo da tallafin da aka yi a boye zai cinye kusan rabin kudin shiga da kasar za ta samu daga arzikin man fetur.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

IMF ta bayyana asarar da za a yi bayan Tinubu ya dawo da tallafi a boye
Hukumar IMF ta ce dawo da tallafin mai a boye da Bola Tinubu ya yi asara ne ga Najeriya. Hoton: Kola Sulaimon, Drew Angerer.
Asali: Getty Images

Asarar da Najeriya za ta yi

IMF ta ce matakin zai laƙume akalla N8.43trn daga cikin N17.7 trn da ake sa ran samu daga cire tallafin man fetur, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wani sabon rahoto da hukumar ta fitar kan Najeriya game da tallafin man fetur, cewar Leadership.

IMF ta ce taso a shafe maganar tallafin mai gaba daya a Najeriya cikin shekaru biyu kacal yayin da gwamnati ke kokarin kawo wasu shirye-shirye.

Najeriya ta na shigo da gas kasar

Sai dai duk da yawan fitar da mai da Najeriya ke yi, ta na shigo da mafi yawan gas kasar saboda ba ta da matattun mai da za su wadaci 'yan ƙasar

A wani bangaren, Bankin Amurka ya ce Najeriya za ta rasa N7bn zuwa N10bn idan ta bukaci shigo da litar 18 zuwa 25 na gas.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi watsa watsa da Gwamnatin Bola Tinubu saboda lafta harajin 0.5% a banki

Wannan martani na hukumar na zuwa ne kusan shekara guda bayan Tinubu ya sanar da janye tallafin mai a kasar.

Shugaban ya sanar da hakan ne a ranar 29 ga watan Mayun 2023 yayin kama rantsuwar mulki a birnin Abuja.

"Tallafi ba zai ci gaba da samar da abin da ake nema ba yayin da tattalin arziki ke sake durkushewa."
"Sai dai mu yi amfani da kudaden wurin inganta matasa da bangaren ilimi da lafiya da kuma zuba hannun jari, tallafi ya tafi."

- Bola Tinubu

Dalilin cire tallafi da Tinubu ya yi

Kun ji cewa Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idrisya ce nan ba da dadewa ba ‘yan Najeriya za su fara ganin amfanin cire tallafin man fetur.

Idris ya ce Tinubu ya ɗauki matakin dakatar da biyan kuɗin tallafin man fetur ne domin amfanin kasar baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.