Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu Ta Ɗauka da Suka Jefa ‘Yan Najeriya a Wahalar Rayuwa

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu Ta Ɗauka da Suka Jefa ‘Yan Najeriya a Wahalar Rayuwa

Abuja - Jama’a da yawa sun yi tunanin za a samu sauki a Najeriya da zarar Mai girma Muhammadu Buhari ya bar karagar mulki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sai dai bayan Bola Ahmed Tinubu ya shiga ofis a karshen Mayun 2023, abubuwa ba su wani canza zani ta fuskar sauyin rayuwa ba.

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

A rahoton nan, Legit Hausa ta jero matakai da ake gani masu daci da gwamnati ta dauka.

Bola Tinubu
Ba a samu saukin rayuwa da Bola Tinubu ya zama shugaban Najeriya ba Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Matakai masu tsauri da Tinubu ya dauka

1. Tinubu ya fara da cire tallafin fetur

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan ‘yan mintuna kadan da canza shugaban kasa a 2023, sai aka ji gwamnatin Bola Tinubu ta tabbatar da cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Naira ta koma gidan jiya, kudin Najeriya ya dawo mafi rashin daraja a duniya

Dama can ba a yi kasafi da wannan kudi ba, wanda hakan ya jawo karin tsadar rayuwa, sai dai gwamnati tana ganin hakan alheri ne.

2. Sabanin ECOWAS, Tinubu da Nijar

Juyin mulkin da aka yi wa Mohammed Bazoum ya fusata kasashen duniya musamman na kungiyar ECOWAS a karkashin Bola Tinubu.

A dalilin haka aka katse alaka da makwabciyar, wannan ya jawo asara sosai ta fuskar kasuwanci da tattalin arziki a jihohin Arewa.

3. CBN ya bar Naira da gantali kasuwa

Sabon gwamnan CBN ya soke tallafin da ake ba Naira domin hana kudin kasashen waje tashi, yin hakan ya jijjiga tattalin arzikin Najeriya.

Masana tattalin arziki sun shaida mana yadda hakan zai taba rayuwar ‘dan Najeriya. Wannan mataki ya jawo Naira ta karye kan Dala.

4. Kwastam da kudin shigo da kaya

An ga tasirin tashin dala kai tsaye wajen shigo da kaya daga ketare inda kwastam ta ke amfani da kimar kudin kasashen waje a farashinta.

Kara karanta wannan

Tafiye-tafiye 20 a watanni 12: Kasashen da Tinubu ya kai ziyara daga zama shugaban kasa

5. Gwamnatin Tinubu ta zo da karin haraji

A karshen nan BBC ta rahoto bankin CBN ya sanar da kirkiro harajin tsaron yanar gizo da na la’adar ajiyen kudi a bankunan kasuwa.

Ko da daga baya an soke na ajiyar, sai dai ana kukan gwamnati tana shirin tatsar har ‘yan hanjin jama’an da ba a kara masu albashi ba.

An kara albashin majalisa a mulkin Tinubu?

Ana da labari cewa rade-radin gwamnatin tarayya ta yi wa Sanatoci da 'Yan majalisa karin albashi a lokacin da ma'aikata suke hamma.

Ja'afar Ja’afar wanda ya fake a Ingila ya ce an kara albashin da ake biyan 'yan majalisa.

Idan zargin ya tabbata, Sanatoci masu samun N13m sun koma tashi da N21m, sannan kudin ‘yan majalisar wakilai ya karu zuwa N13m.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng