Gwamnati Za Ta Dawo da Lantarki a Garuruwan da Aka Yi Shekaru Babu Wuta a Sokoto

Gwamnati Za Ta Dawo da Lantarki a Garuruwan da Aka Yi Shekaru Babu Wuta a Sokoto

  • Gwamnatin tarayya ta ayyana kudirin dawo da lantarki ga ƙananan hukumomin da suka shafe shekaru ba wuta a jihar Sokoto
  • Ministan makamashi ne, Adelabu Adebayo, ya bayyana haka yayin wata ziyara da gwamnan jihar, Ahmed Aliyu, ya kai masa.
  • Tuni aka tura ma'aikata domin duba halin da wuraren ke ciki tare da bayyana irin matakan da za su dauka wurin kammala aikin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Gwmantin tarayya ta yi alkawarin dawo da wutar lantarki a kananan hukumomi guda takwas a Sokoto bayan shafe sama da shekaru 10 ba wuta.

Sokoto governor
Gwamantin tarayya ta tura wakilai Sokoto domin gyaran lantarki. Hoto: Ahmad Aliyu Sokoto
Asali: Facebook

Ƙananan hukumomin za su samu tagomashin ne bayan gwamnan jihar, Ahmed Aliyu, ya koka kan lamarin yayin da ya kai wa ministan makamashi, Adelabu Adebayo ziyara.

Kara karanta wannan

'Akwai manyan da ke yi wa gwamnatina makarkashiya', Gwamnan APC ya koka

Rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa tuni an tura ma'aikata da za su gabatar da bincike domin dawo da wuta a yankunan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabin jami'in ma'aikatar wuta ta kasa

A lokacin da yake jawabi a Sokoto, Mustafa Baba Umarah, jami'in ma'aikatar makamashi ta kasa ya ce za su bincika duk matsalolin da suke kananan hukumomin domin daukan mataki.

Jami'in ya ce gwamnati ta dukufa wurin tabbatar da cewa dukkan 'yan Najeriya sun samu wutar lantarki.

Maganar Kwamishinan makamashin jihar Sokoto

Kwamishinan makamashi na jihar Sokoto, Sanusi Dan Fulani, ya ce kokarin da gwamnatin jihar ke yi wurin samar da wuta a kauyuka yana cikin alkawarin da gwamnan ya yi na inganta rayuwar mutanen karkara.

Kwamishinan ya ce samar da wuta a yankunan yana da muhimmanci sosai musamman wurin habaka tattalin arziki da noma.

Kara karanta wannan

A tuna da matattu: Sanata a Kano ya rabawa 'yan mazabarsa likkafani da tukwanen kasa

Garuruwan da za su samu wutar lantarki

Ya kuma yi kira na musamman ga mazauna yankunan wurin bada hadin kai domin tabbatar da nasarar aikin, cewar jaridar Leadership

Kananan hukumomi da za su amfana da aikin sun hada da Isa, Sabon Birni, Goronyo, Wurno, Rabah, Gada, Illela da Gwadabawa.

Rashin ruwa ya yi kamari a Sokoto

A wani rahoton, kun ji cewa matsalar rashin wuta ta yi katutu a jihar Sokoto wanda hakan har ya fara tasiri wurin rage ayyukan da kamfanoni da masana'antu ke yi a fadin jihar.

Matsalar ta fara bazarana ga masu kamfanin ruwan leda, masu buga bulo, masu gidan wanka da bahaya da masu wankin mota sakamakon yanke musu ruwa da hukuma ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel