Alhazan Jihar Osun Sun Gudanar Da Zanga-Zanga a Saudiyya Kan Rashin Ingancin Abinci

Alhazan Jihar Osun Sun Gudanar Da Zanga-Zanga a Saudiyya Kan Rashin Ingancin Abinci

  • Haƙurin Alhazan jihar Osun ya ƙare kan irin abincin da ake ciyar da su da shi a ƙasa mai tsarki ta Saudiyya
  • Alhazan dai sun fusata inda suka ɓarke da zanga-zanga kan rashin ingancin abincin da ake basu tun da suka isa Saudiyya
  • Hankula sun kwanta bayan manya sun shiga cikin lamarin inda suka ba Alhazan haƙuri su daina zanga-zangar

Saudiyya - Alhazan jihar Osun da su ke gudanar da aikin Hajji a ƙasa mai tsarki sun gudanar da zanga-zanga kan abincin da hukumar jindaɗin Alhazai ta jihar Osun ke ba su a Saudiyya.

A cikin wani bidiyo da jaridar The Punch ta samo a ranar Lahadi, an nuna Alhazan suna zubar da abincin da aka basu a ƙofar ɗaki mai lamba 211, wanda nan ne Amirul Hajj na jihar, Dr. Maroof Ishola yake a ciki.

Kara karanta wannan

Amarya Da Kannen Mijinta Sun Kubuta Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane a Jihar Kwara

Alhazan jihar Osun sun yi zanga-zanga a Saudiyya
Alhazan sun raina ingancin abincin da ake ba su (Ba alhazan ba ne a cikin wannan hoton) Hoto: Punchng.com
Asali: UGC

A cewar majiyoyi, Alhazan sun yi ta ƙorafi kan rashin ingancin abincin da ake basu tun da suka iso ƙasa mai tsarki.

Alhazan sun fusata kan rashin ingancin abincin da ake basu

An tattaro cewa hankula sun ƙara tashi ne kan jindaɗin Alhazan bayan wasu daga cikinsu sun ziyarci sansanin Alhazan jihar Legas inda suka fahimci cewa ana basu abinci mai rai da lafiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alhazan dai sun fara zanga-zangar ne a yammacin ranar Asabar a harabar otal ɗinsu da ke a birnin Madina, bayan masu dafa abincin sun kawo musu abincin da suka raina ingancinsa.

A cikin bidiyon zanga-zangar, wani daga cikin Alhazan ya bayyana cewa:

"Ba za mu karɓi abincin da ake bamu ba. Muna nan a ƙofar ɗakin Amirul Hajji na jihar Osun. Ba za mu karɓi abincin da ake ba mu ba. Abincin bai da inganci, ba za nu ci gaba da cin irinsa ba, bayan mun biya maƙudan kuɗaɗe saboda wannan aikin Hajjin.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Ta'adda Sun Kashe Basarake Bisa Kuskure, Sun Sace Mutum 3 a Wata Jihar Arewa

Daga baya hankula sun kwanta bayan Ataoja na Osogbo, Oba Jimoh Oyetunji, ya sanya baki inda ya buƙaci Alhazan da su dakatar da zanga-zangar.

Ga bidiyon zanga-zangar nan ƙasa:

Maniyyata Mata 75 Sun Kare a Gadon Asibiti a Saudiyya

A wani labarin kuma, wasu daga cikin maniyyata mata na wannan shekarar sun tsinci kansu a gadajen asibiti a biranen Makkah da Madina na ƙasa mai tsarki.

Hukumar NAHCON ta bayyana cewa an kwantar maniyyatan ne a asibiti saboda juna biyun da su ke ɗauke da shi. Maniyyatan dai sun yi fatali da gargaɗin hukumar na kada su je aikin Hajjin tun da suna da juna biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel