IMF Ya Kuma Zugo Shugaba Tinubu a Cire Tallafin Lantarki Ana Kukan Kuncin Rayuwa

IMF Ya Kuma Zugo Shugaba Tinubu a Cire Tallafin Lantarki Ana Kukan Kuncin Rayuwa

  • Asusun bada lamuni na duniya (IMF) ya yi sabon kira ga gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu kan cire tallafi a Najeriya
  • IMF ya yi kiran ne kan kammala cire tallafin lantarki da man fetur tare da bayyana lokacin da ya kamata a cire su
  • Wannan kiran yana zuwa ne bayan halin kunci da aka shiga bayan cire tallafin mai da gwamnatin ta yi a shekarar 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Asusun bada lamuni na duniya (IMF) ya yi kira ga gwamnatin tarayya kan kammala cire tallafi man fetur da wutar lantarki.

IMF Tinubu
IMF ta ce tallafin fetur da lantarki bai amfanar da talakawa. Hoton: Kola Sulaimon, Drew Angerer.
Asali: Getty Images

Sai dai a wannan karon IMF ya yi kiran tare da saka sharadi kan lokacin da ya kamata a cire tallafin.

Kara karanta wannan

"Wannan ai sata ce," NLC ta magantu kan karin kudin wutar lantari a Kogi

Yaushe IMF ke so a cire tallafi?

Rahoton da Daily Trust ta fitar ya nuna cewa IMF ya ce gwamnatin ya kamata ta cire tallafin ne da zarar ta magance matsalolin hauhawar farashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asusun bada lamunin ya kara da cewa a yanzu haka gwamnatin tarayya da dauki hanyar magance matsalolin hauhawar farashin kayayyaki.

Shirin gwamnati na cire tallafi

A cewar asusun, gwamnatin Najeriya ta fara shirye-shiryen raba kudade wanda sune za su magance matsalolin da Najeriya ke ciki.

Wani rahoto da cibiyar Bretton Wood ta fitar ya nuna cewa kimanin mutane miliyan 60 ko gidaje miliyan 15 za su amfana da tallafin kuɗin.

Za a samar da tallafin kudin ne cikin wata hadaka tsakanin gwamnatin Najeriya da bankin duniya.

Kuma za a cigaba da raba tallafin ga wadanda suka cancanta cikin gaggawa da bin hanyoyin da suka dace na hana hauhawar farashi

Kara karanta wannan

Kayayyaki za su kara tsada a Najeriya, an kara harajin shigo da kayan kasar waje

Saboda haka IMF ya ba Najeriya shawarin cire tallafi man fetur da na lantarki da zarar an kammala raba kudin, rahoton the Cable.

IMF ya kafa dalilli kan cire tallafi

Babban dalilin da IMF ya bayar kan cire tallafin man fetur da lantarki shine gwamnati na saka tallafin ne ba bisa ka'ida ba.

IMF ya ce tallafin yana jawo kashe kudade masu yawa ga gwamanti kuma bai isa ga talakawan da ya kamata su samu.

Halin da Najeriya ta shiga bayan cire tallafi

Wannan kira na IMF dai hana zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke dandana kudarsu kan cire tallafin man fetur.

Dadin dadawa kuma janye tallafin wutar lantarki na cigaba da jawo kungiyoyin kwadago na zanga-zanga da rufe ofisoshin kamfanonin raba wuta.

IMF ta shawarci Tinubu kan tallafi

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar IMF ta yi magana kan muhimmancin cire tallafin mai gaba daya da kuma tabbatar da cire na wutar lantarki.

Kara karanta wannan

IMF ta damu kan yadda Tinubu ya dawo da tallafin mai a boye, ta jero matsaloli

Hukumar ta shawarci gwamnatin da cewa ya kamata ta cire dukkan tallafin saboda yawan kudade da ta ke kashewa kuma ribar bata isa ga talakawa.

Muhammad Malumfashi, babban editan sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel