Gwamnatin Kano ta Dakatar da Wata Likita Saboda Barin Mara Lafiya a Bakin Mutuwa

Gwamnatin Kano ta Dakatar da Wata Likita Saboda Barin Mara Lafiya a Bakin Mutuwa

  • Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da wata likita mai wankin koda a asibitin koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase da aka fi sani da asibitin Nassarawa
  • Shugaban hukumar kula da manyan asibitocin Kano, Dr. Mansur Mudi Nagoda ne ya bayyana dakatar da likitar saboda kin zuwa wanke kodar wani mara lafiya
  • Ya bayyana cewa gwamnatin Kano ta samar da dukkanin asibitocin jihar saboda haka ba za su bari ma'aikata suna watsar da rantsuwar aiki ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano-Babban sakataren hukumar kula da asibitoci a Kano, Dr. Mansur Mudi Nagoda, ya dakatar da wata likitar asibitin koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase, watau asibitin Nassarawa da ta ki zuwa aiki.

Kara karanta wannan

Operation kauda badala: Hisbah ta damke maza da mata 20 suna wanka tare a Kano

Kakakin hukumar, Hajiya Samira Sulaiman ta tabbarwa Legit Hausa cewa Dr. Nagoda ya ce da bacin rai likita ta bar bakin aiki lokacin da marasa lafiya ke bukatar ta.

Gwamnatin Kano ta dakar da likita a Kano
An dakatar da likitar da ta ki zuwa wankin kodar mara lafiya a Kano/ An sa wannan hoto ne don misali Hoto: Laylabird
Asali: Getty Images

An gano likitar da aka sakaye sunanta ba ta zo aiki ba ne lokacin da aka kawo mai matsalar koda dake bukatar kulawa, amma aka neme ta sama ko kasa, kuma hakan ya galabaitar da mara lafiyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai kayan aiki a Kano,” Dr. Nagoda

Shugaban hukumar kula da manyan asibitoci a Kano, Dr. Mansur Mudi Nagoda ya ce gwamnati ta samar da kayan aiki a asibitocin jihar.

Ya ce saboda haka ba za su lamunci wadanda ba sa zuwa aikinsu a kan lokaci ba ko wasarere da kula da lafiyar al'umma.

Kano: An dakatar da likita daga aiki

Shugaban ya bayyana haka ne yayin da ya aka dakatar da wata likita mai kula da na’urar wankin koda a asibitin Nassarawa da ke jihar.

Kara karanta wannan

"Daurarru 400 a Kano ba su san makomarsu a gidan yari ba," Inji 'Yan Sanda

Gwamnatin Kano ta ce bai kamata saboda mace ta na da aure ta ki zuwa aikinta na dare a asibiti ba, kuma an dakatar da likitar da ta ki kwana a asibiti har sai ta bayar da gamsashshiyar amsa.

Sanata Hanga ya raba kaya ga makabartu

A baya mun ba ku labarin cewa Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Rufa'i Sani Hanga ya rarraba kayan binne gawa cikin har da tukwanen kasa 2,000 da likkafani yadi 10,500.

Bayan sukar matakin ne ya ce da kudin aljihunsa ya dauki nauyin bayar da tallafin ba da kudin gwamnati ba, saboda haka bai kamata a rika sukar sa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel