Tashin Hankali a Jihar Kwara Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Kashe Basarake, Suka Sace Mutum 3

Tashin Hankali a Jihar Kwara Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Kashe Basarake, Suka Sace Mutum 3

  • Rahoton da muke samu daga jihar Kwara ya bayyana cewa, wasu tsagerun ‘yan bindiga sun sace basarake tare da sace wasu mutane
  • Hakan ya faru ne a ranar Juma’a, inda aka bayyana yadda suka aikata mummunan barnar a wani gidan mai
  • Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da bincike da bin diddigin inda ‘yan ta’addan suka boye don ceto wadanda aka sace

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kwara - Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun yi awon gaba da mutane uku tare da kashe wani basarake a yankin Iwo da ke karamar hukumar Isin (LGA) ta jihar Kwara, bayan sun afka cikin garin, Channels Tv ta ruwaito.

An tattaro cewa ‘yan bindigar sun kai hari ne a wani gidan mai da ke unguwar Sabaja da ke garin da misalin karfe 9 na daren ranar Juma’a inda suka yi awon gaba da manaja da wani mai gadi da kuma wani limamin cocin Christ Apostolic Church (CAC).

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Tona Shirin ‘Yan Ta’adda a Lokacin Bukukuwan Sallah a Najeriya

An dai ce harin ya fara ne da harbe-harbe, inda mazauna yankin suka fara gudun tsira. An bayyana cewa, an kashe wani babban basarake na Sabaja, mai suna Cif Raphael Adewuyi, a lokacin da harsashi da ya bi dakinsa.

Yadda aka kashe basarake tare da sace wasu mutum 3 a Kwara
'Yan sandan Najeriya a lokacin kula da aiki | Hoto: Aminu/GettyImages
Asali: Getty Images

An tabbatar da faruwar lamarin

Shugaban kwamitin TIC a yankin, Isin Tunde Fadipe a ranar Asabar ya tabbatar da cewa harsashi ne ya kashe basaraken garin a lokacin da lamarin ya faru.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

“Mutane uku da suka hada da manajan gidan mai, mai gadi da wani limamin coci an yi garkuwa da su a lokacin da lamarin ya faru, yayin da wani basarake ya gamu da harbin bindiga a gidansa yayin da ake barnar.”

Shirin da ake na tabbatar da kubutar da wadanda aka sace

Fadipe ya bayyana cewa kwmaitin tare da hadin gwiwar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun hada kan jami’ai domin bin sawun ‘yan bindigar tare da kubutar da mutane ukun da aka sace.

Kara karanta wannan

Neja: Bene Ya Ruguje Tare Da Kashe Yaro Dan Shekara 15, Gwamnati Ta So Rushe Benen Kafin Yanzu

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, SP Okasanmi Ajayi, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce masu garkuwa da mutanen tabbas sun yi garkuwa da mutane uku a gidan mai da ke unguwar Iwo a daren Juma’a, rahoton Tribune Online.

Ana yawan samun hare-haren ‘yan bindiga a yankuna daban-daban na Najeriya, musamman a yanayin da tsaro ke kara tabarbarewa..

A lamari irin wannan, wasu 'yan ta'adda sun kashe wani matashi mai kananan shekaru a wani yankin jihar Bauchi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel